Wasu fusatattun matasa sun jibge gawar mutum sama da 20 da aka kashe a wani sabon hari da aka kai kauyen Yelwan Zangam da ke wajen garin Jos, a Gidan Gwamnatin Jihar Filato.
Dattawan kauyen na Yelwan Zangam, sun ce an kashe musu mutum 37 a sabon harin da aka kai daga tsakar dare zuwa wayewar garin Laraba, inda maharan suka kona wasu daga cikin mamatan dakunan da suka boye.
- Yadda Daruruwan Likitoci Ke Tururuwar Barin Najeriya
- Sabon Harin Jos: An sa dokar hana fita ta sa’a 24
Bayan harin ne daruruwan matasa da matan kauyen, wanda mazaunansa ’yan kabilar Anaguta ne, suka gudanar da zanga-zanga, tare da neman gwamnati ta dauki mataki ta hukunta maharan.
Da farko mutanen garin sun kai mamatan dakin ajiyar gawa da ke Asibin Filato, amma daga baya fusatattun matasan suka je suka kwashe gawarwakin a mota zuwa harabar Majalisar Dokokin Jihar, da ke kusa da asibitin; Daga suka wuce da su suka jejjera a kofar gidan gwamnatin.
Mutanen da aka kashe a harin sun hada da mata da kananan yara.
Wasu daga cikin iyalan wadanda sabon harin ya yi ajalinsu na zargin Fulani makiyaya ne suka kai musu farmakin, amma al’ummar Fulanin Jihar ta Filato sun yi fatali da zargin.
Wasu kuma na zargin harin na da alaka da rikicin fili da ke tsakanin mazauna kauyen na Yelwan Zangam da makwabtansu, wato kauyen Yelwan Mista Bow.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ta tabbatar da harin, amma ba ta yi karin bayani a kai ba game da yawan mutanen da lamarin ya ritsa da su ko irin asarar dukiyoyi da aka yi.
Amma a nata bangare, Gwamnatin Jihar, wadda ta sanya dokar hana fita gaba daya da Karamar Hukumar Jos ta Arewa ta ce akalla mutum 10 da ake zargi da hannu a harin sun shiga hannu.