Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce ya yi odar sabbin takardun kudi guda miliyan 500 bayan sauya takardun N200, N500 da kuma N1,000.
Mataimakiyar Gwamnan CBN Mai Kula Da Daidaiton Harkokin Kudi, Aisha Ahmad, ce ta sanar da haka a lokacin da take amsa tambayoyi kan sabuwar dokar bankin na takaita amfani da tsabar kudi a ranar Alhamis.
- NAJERIYA A YAU: Anya ‘Yan Najeriya Za Su Gamsu Da Tsarin Takaita Amfani Da Tsabar Kudi?
- ’Yan bindiga sun kashe dan kasar China a Zamfara
“Abin da muka yi oda daga kamfanin buga kudi shi ne sabbin takardun Naira guda miliyan 500,” in ji ta.
Ta bayyana haka ne bayan da farko ta shaida wa ’yan Majalisar Wakilai cewa ba ta da masaniyar hakikanin yawan sabbin takardun kudin da aka buga.
Mataimakiyar Gwamnan CBN din ta kuma shaida musu cewa babu siyasa a sauya takardun kudin da kuma tsarin takaita amfani da kudi da CBN ya yi, kamar yadda ake rade-radi.
Ta fadi haka ne a yayin da take amsa tambayar Dan Majalisa Chinedu Obidigwe, game da ko sabbin tsare-tsaren bankin na takaita amfani da tsabar kudi da sauya takardun kudi suna da alaka da zaben 2023.
Idan ba a manta ba, Aminiya ta kawo rahoton cewa Majalisar Wakilai ta nemi ganawa da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne, don ganin bankin ya kara yawan tsabar kudin da ’yan Najeriya za su iya cirewa a karkashin sabuwar dokar.
Bayan samun wasikar cewa Emefiele ba zai samu zuwa ba saboda yana kasar waje domin duba lafiyarsa, Majalisar ta amince ta yi zaman da mataimakiyar tasa.
A jajibirin ganawar tasu ne CBN ya fitar da sanarwar kara yawan tsabar kudin da za a iya cira a kasar da ninki biyar.
Bisa sabuwar sanarwar, CBN ya kayyade cire N500,000 a mako ga daidaikun mutane, kamfanoni kuma N5,000,000 a mako.
A baya, bankin ya kayyade wa daidaikun mutane N100,000 ne a mako, kamfanoni kuma N500,000.
Sabuwar dokar takaita amfani da tsabar kudin dai za ta fara aiki ne a ranar 9 ga watan Janairu, 2023.