✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sabbin mutane 15 da suka ci zaben gwamnoni

Takwas daga cin sabbin gwamnonin 'yan APC ne, 1 dan NNPP, sai bakwai daga PDP

Kawo yanzu mutum 15 ne suka daga jam’iyyu daban-daban suka lashe zabe domin zama gwamna a karon farko a jihohin Najeriya.

Takwas daga cikin sabbin gwamnonin sun ci zaben ne a karkashin inuwar Jam’iyyar APC, 1 a NNPP sai wasa bakwai a babbar jam’iyyar adaawa ta PDP.

Ga jerin sunayen sabbin gwamnonnin:

Sabbin gwamnoni daga APC

 1. Ahmad Aliyu  SAKKWATO
 2. Bassey Otu — KUROS RIBA
 3. Dikko Umar Radda  KATSINA
 4. Francis Nwifuru  EBONYI
 5. Hyacinth Alia   BINUWAI
 6. Uba Sani  KADUNA
 7. Umaru Bago  NEJA
 8. Umar Namadi — JIGAWA

Sabon gwamna daga NNPP

 1. Abba Kabir Yusuf (NNPP) — KANO

Sabbinoni daga PDP

 1. Caleb Mutfwang (PDP)  FILATO
 2. Dauda Lawal Dare (PDP)  ZAMFARA
 3. Kefas Agbu (PDP)  TARABA
 4. Sheriff Oborevwori (PDP)  DELTA
 5. Siminialayi Fubara (PDP) — RIBAS.
 6. Umo Eno (PDP)  AKWA IBOM.

A ranar 18 ga watan Maris da muke cikin ne Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta gudanar da zaben gwamnoni a jihohi 28 da ke kasar mai yawan jihohi 36 da kuma babban birnin Tarayya.

Sauran johohi takwa da ba a gudanar da zaben ba, nasu zaben gwamnonin na gudana ne a lokuta daban-daban, saboda wasu dalilan da suka sa zaben nasu ya bambanta.

A birnin tarayya dai ba a gwamna.