Sabbin likitoci 22 da Gwamnatin Jihar Gombe ta dauka na barazanar barin aikin saboda gaza fara biyan su albashi, kusan wata biyar bayan daukarsu aikin.
Likitocin dai, wadanda sabbin kyankyasa ne daga Jami’ar Jihar Gombe, a dauke su aiki ne a watan Yuli.
- ‘’Yan bindiga suna aikata ta’addanci amma ba ’yan ta’adda ba ne’
- Mun bankado sunan jariran da ake biya albashi daga lalitar Borno – Zulum
Da yake zantawa da Aminiya a madadin sauran likitocin saboda uku daga cikin 22 din sun tafi, Dokta Kabiru Abdullahi, ya ce gwamnati ta shelanta daukarsu aiki a cikin asibitin kuma har ta ba su gidajen kwana a asibitin, kamar yadda doka ta tanadar.
A cewarsa, lokacin da suka ga ana ta hanya-hanya da batun biyansu albashi, sun bi duk hanyoyin da suke ganin za su bulle dan neman mafita amma lamarin ya ci tura.
Ya ce hakan ne ya sa suke kokarin sanar da duniya halin da suke ciki ko gwamnati za ta ji kokensu.
Dokta Kabiru, ya ce wani lokaci abin da za su ciyar da iyalansu ma ya kan gagaresu.
Ya ce yanzu haka likitoci uku a cikin su sun tafi kuma, su ma suna kan hanya muddin gwamnati ba ta dauki matakin biyansu hakkokinsu ba.
Har ila yau, ya koka kan yadda ba sa samun horon da ya dace domin yin aikin daga kwararrun likitoci da suka jima suna aiki.
Likitocin sun kuma yi barazanar cewa muddin gwamnati ba ta magance matsalar ba nan da wata daya za a neme su a rasa kuma wasu sabbin likitocin ba za su yarda su zo su yi aiki a asibitin ba.
Shi ma da yake tsokaci a kai, wani daga cikin likitocin, Dokta Ahmad M. Ibrahim, ya ce a lokacin da suka fara aiki a asibitin, an magance matsalar karancin likitoci da mace-macen marasa lafiya, amma sai ga shi duk da haka an musu rikon sakainar kashi.
Aminiya tayi kokarin jin bangaren gwamnati ta bakin Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dokta Habu Dahiru, amma duk kokarin wakilinmu ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.