✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ruwan teku ya koro kunkuru mai kai biyu waje

Sai dai masana sun ce a kan sami irinsu.

An sami wani karamin kunkuru mai kai biyu a Tsibirin Hatteras da ke gabar teku a Jihar Karolina ta Arewa (North Carolina) a kasar Amurka.

An gano kunkurun mai kai biyu ne a bakin teku a karo na biyu a ’yan makonnin da suka gabata.

Shafin Facebook na Cape Hatteras National Seashore ya wallafa bidiyon kunkurun bayan gano wannan karamar halitta a gabar tekun North Carolina.

Wani masanin ilimin halittu, Will Thompson ya ce irin wadannan halittu suna da yawa fiye da yadda ake zato.

Thompson ya ce, “Gaba daya kananan halittu da ake kyankyashewa kamar kunkuru a Cape Hatteras National Seashore da duniya baki daya, ba sabon abu ba ne a gan su da kai biyu.”

“Muna ganin nakasassu a halittu a kowace shekara a zababbun wuraren da suke gabar teku, a yayin da ake aikin hakar rami.”

Ya tabbatar da cewa, halittar kunkurun ba wani abin mamaki ba ne.

Thompson ya ce, kyankyasar da alama an yi ta ce cikin koshin lafiya kuma an fitar da kwan ba tare da wata matsala ba a cikin tekun.

Wannan shi ne karo na biyu cikin ’yan makonni da aka ga kunkuru mai kai biyu a Amurka.

An kuma gano wani abu a Edisto Beach State Park a tsibirin Edisto a Kudancin Karolina.

Jami’ar wurin shakatawa na Jihar Karolina ta Kudu a cikin wata sanarwa a Facebook ta bayyana yadda jami’an da suke aikin tono kasa kwana uku zuwa biyar suka yi nasarar gano kunkurun.

Za su iya kiyasta kyankyasar da suka fito daga bawonsu da wadanda suka mutu don tantance yuwuwar habakar rayuwarsu a masaukinsu kamar yadda ya kamata.

Yayin da suke haka daya daga cikin masaukan kunkurun, sun samu wadanda aka kyankyashe guda uku a cewar sanarwar, amma dayansu ya fi fice.

“Yayin da suke tantancewa a ranar Laraba da ta gabata, masu aikin sa-kai sun samu
kyankyasar kunkuru masu rai a tekun uku, har yanzu suna cikin dakin bincike, amma daya da aka kyankyashe ya fito waje saboda yana da kai biyu!

“An taba gano wasu da aka kyankyashe masu kai biyu a Jihar Karolina ta Kudu a shekarun da suka gabata, amma wannan ne na farko da ayarin jami’ai masu aikin hakar suka gano a Edisto Beach State
Park.

“Bayan fitar da hotunan, an gano kyankyasar tare da wasu biyun da aka samu a cikin teku.”

An saki kunkurun uku a cikin tekun bayan da jami’an suka dauki lokaci da sababbin kyankyasar da ba su mutu ba a lokacin.