Aƙalla mutum uku sun rasu, yayin da wasu bakwai suka jikkata, bayan da wani gini ya rufta sakamakon mamakon ruwan sama a ƙaramar hukumar Nangere da ke Jihar Yobe.
Aminiya ta ruwaito cewar, Iftila’in ya faru ne a Tsohon Gari da ke hedikwatar ƙaramar hukumar Nangere a ƙarshen wannan makon.
- Tsohon Babban Hafsan Tsaro Ibrahim Ogohi ya rasu
- Shugabar Ƙaramar Hukuma ta ƙaddamar da yaƙi da cutar Kwalara a Gombe
Majiya daga yankin ta ce sama da gidaje 50 ne suka lalace, lamarin da ya sanya mutane da dama rasa matsugunansu.
Wani mazaunin yankin, Shuwa Adamu, ya shaida wa Aminiya cewar ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da iska ne ya yi sanadin rushe gidajen.
“Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 9 na safe lokacin da yawancin mazauna yankin ke shirin fita kasuwa kamar kullum.
“Akalla shaguna da gidaje 50 ne suka lalace, sai kuma wani yaro ɗan shekara bakwai da ya rasu.
“Jami’an Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe sun tantance adadin asarar da aka yi a yankin,” in ji shi.
Wata mazauniyar yankin, mai suna Halima ta ce ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya yi ajalin mutum uku tare da lalata kadarori da dama.
“Sama da gidaje 50 ne suka lalace yayin da mutum uku ciki har da wani yaro ɗan shekara bakwai, suka mutu.
“Mutanen da suka rasa gidajensu a halin yanzu suna tare da danginsu,” in ji ta.
Da yake mayar da martani kan lamarin, sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (Yosema) Dokta Goje Muhammad, ya jajanta wa wadanda abin ya shafa.
Ya ce hukumar ta biya kuɗin kula da lafiyar waɗanda suka jikkata da ke babban asibitin Nangere.
Kazalika, ya ce an sallami waɗanda suka jikkata baki ɗaya daga asibitin.