Wani ginin bene mai hawa biyu ya fadi a garin Bukur da ke Karamar Hukumar Jos ta kudu, sakamakon wani ruwa da aka ka yi kamar da bakin kwarya.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 8:30 na safe a cewar wani mazaunin garin wanda lamarin ya faru a idonsa.
- Wani matashi ya fado daga bene yayin da ya ke sharar bacci
- Mutum 4 sun mutu sanadiyyar rushewar gini a Delta
Benen mai hawa biyu, wurin harkar kasuwanci ne a inda ginin ke dauke da kantin sayar da kayyakin bukatun yau da kullum, da kuma dakin ajiyar kayayyaki.
A lokacin da wakilinmu ya ziyarci wurin, ya taras da jami’an Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA, da kuma Hukumar Kashe Gobara suna ta aikin wadanda suka makale a baraguzan ginin.
Sai dai mai benen da ya fadi, Mista Pam ya ce, a saninsa babu wani wanda ke cikin ginin, shi kadai ne a lokacin da ginin ya fadi.