Fiye da mutum dubu 500 ne ambaliyar ruwa ta shafa a Habasha, yayin da wasu yankunan kasar suka ce an samu ruwan saman da ba a taba ganin irinsa ba cikin shekara 100, kamar yadda Ministan Ruwa, Seleshi Bekele ya bayyana.
Ministan ya ce ambaliyar ruwan ta raba kimanin mutum dubu 200 da muhallansu a larduna biyar daga cikin lardunan kasar guda goma.
- Basussukan Najeriya: Ko kun san nawa ake bin ko wannenku?
- A gaggauta korar hafsoshin tsaro —Dattawan Arewa
Ambaliyar ta kuma hallaka dabbobi tare da barnata amfanin gona da lalata gidaje da rusa ababen more rayuwar al’umma, wadda ba a taba ganin kwatankwacinta ba.
Yayin da lamarin ke kara muni a ’yan kwanakin nan, gwamnatin kasar ta fara rarraba kayayyakin agaji a wuraren da ambaliyar ta shafa ta hanyar amfani da jirage masu saukar ungulu.
Kasar Sudan mai makwabtaka da Habasha ma ta fuskanci mummunan ambaliyar ruwa a bana.
Ambaliyar ta faru ne sakamakon sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka gani a daminar bana, inda yawan ruwan Kogin Nilu ya yi torokon da bai taba yi ba a cikin karnin nan.