Ruwan famfo a yankin Kubwa da ke babban birnin tarayya wato Abuja, ya fara dawowa bayan shafe kwanaki 13 da daukewa.
Daukewar ruwan ta biyo bayan wani aikin gaggawa da ya shafi madatsar ruwa ta Usuma da ke garin na Abuja.
- An yi jana’izar Kakar tsohon Shugaban Amurka, Barack Obama
- Ganduje ya fitar da N8.9bn na gina Gadar Sama a Hotoro
- Buhari zai tafi Landan ganin Likita
- An yi wa Buhari zanga-zanga a Landan
Wannan lamari ya jefa al’ummar yankin cikin wani mawuyacin hali wanda a dole suka koma saye wajen ‘yan ga ruwa.
Wasu mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa, tun daga yammacin ranar Talata ruwan ya fara dawowa har zuwa safiyar ranar Labara.
Sai dai wasu daga cikin mazauna yankin har yanzu ruwan bai dawo a yankunansu ba kamar yadda suka shaida wa wakilinmu.
Wata majiya daga Hukumar Rarraba Ruwan Famfo ta Abuja, ta bayyana cewa matsalar rashin isar ruwan ko ina ta faru ne a sakamakon lalacewar bututun ruwa da ke kauyen Chikakuri.
Majiyar ta kara da cewa, an yi asarar ruwa mai yawan gaske, inda aka dinga tura shi zuwa daji don gudun barna.
Kazalika, majiyar ta ce suna ci gaba da aiki tukuru don ganin ruwan ya isa zuwa yankunan Gwagwalada, Gudu da kuma yankin Jami’ar Abuja.