✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rundunar ’Yan Sandan Nasarawa na fama da karancin kayan aiki – Kwamishina

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Nasarawa Malam Sadik Abubakar Bello ya ce rundunarsa tana fama da karancin kayayyakin aiki. Kwamishinan ya fadi haka ne a lokacin…

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Nasarawa Malam Sadik Abubakar Bello ya ce rundunarsa tana fama da karancin kayayyakin aiki.

Kwamishinan ya fadi haka ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin sauraran koke-koke da tsaro na Majalisar Dokokin Jihar don amsa tambayoyin da suka shafi tsaro a jihar. Ya ce issasun kayayyakin aiki musamman motoci da inganta jin dadin ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro a jihar za taimaka nesa ba kusa ba wajen dakile ayyukan batagari da suke son zama ruwan dare a jihar.

Ya ce “A gaskiya muna matukar bukatar karin motocin sintiri da inganta jin dadin ’yan sanda a jihar nan. Muna fuskantar rashin wadatattun ’yan sanda don haka ne muke aiki da ’yan banga don cike gibin karancin ’yan sanda da muke fuskanta a yanzu.”

Kwamishinan ya ce duk da gwamnatoci a dukan matakai suna kokari wajen inganta aikin ’yan sanda a kasar nan, amma har yanzu akwai bukatar a kara tallafa musu a wannan bangare, inda ya bukaci majalisar ta isar da wannan sako ga gwamnatocin.

Ya bukaci al’ummar jihar su rika bai wa ’yan sanda ingantattun bayanai da za su taimaka musu wajen dakile ayyukan batagari, kuma ya bukaci su kasance masu bin doka da oda da tabbatar da zaman lafiya a tsakaninsu da makwabtansu ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba, don ci gaban jihar.

Da yake mayar da jawabi shugaban kwamitin kuma dan majalisa mai wakiltar Lafiya ta Arewa Alhaji Ibrahim Alkali ya tabbatar wa kwamishinan cewa majalisar za ta mika koke-kokensu ga gwamnatin jihar da ta tarayya don tabbatar an share musu hawaye cikin lokaci.

Ya ce majalisar ta gayyato shi ne don tattauna yadda za a fuskanci kalubalen tsaro domin kawo karshen ayyukan miyagun mutane a sassan jihar.

In za a tuna a kwanakin baya wadansu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun sace wani sanannen mai ba da maganin gargajiya da ake kira Abraham Nakowa da ke kauyen Moro a Karamar Hukumar Akwanga a jihar inda daga bisani suka kashe shi.