Rundunar Dakarun Sojin Sama ta Operation Hadarin Daji, ta yi wa ‘yan ta’adda ruwan wuta a Gabashin yankin Wagini na jihar Katsina, inda ta samu nasarar kashe ‘yan bindiga bila adadin.
Cikin sanarwar da Babban Jami’in sadarwa na rundunar tsaro ta kasa, Manjo Janar John Enenche ya sanya wa hannu, ya ce an kai wa ‘yan ta’addan harin na bazata a ranar 8 ga watan Oktoba.
Ya ce an samu nasarar cin galaba a kan masu tayar da kayar bayan ta hanyar amfani da jiragen yaki na sama bayan samun wasu bayan sirri da bincike da aka gudanar ta karkashin kasa.
Manjo Janar Enenche yayin bayar da tabbaci kan nasarar da aka samu wajen bincike, ya ce an gano wani sansanin mai dauke da daruruwan ‘yan bindiga da shanu da dama da suka sato musamman a kauyukan Katsina da Zamfara.
Y ace ganin haka ya sanya aka rika yi sansanin ruwan wuta daga sama kuma aka samu nasarar kawar da ‘yan bindiga da dama daga doron kasa tare da tarwatsa wani sashe na sansanin.