Rundunar sojin Najeriya ta kafa kwamiti da zai bincike zargin da T Y Danjuma ya yin a cewa rundunar na yin son kai a wajen gudanar da aikin tsaro.
Kwamitin wanda aka kafa karkashin jagorancin manjo janar John Nimyel mai ritaya zai gudanar da bincike ta hanyar zagaya wa musammam Jihar Taraba da wasu jihohin tare da tattaunawa da wadanda abin ya shafa da kuma.
Babban hafsan rundunar sojin, Laftanar Janar Tukur Buratai ya hori kwamitin da suka yi aiki da gaskiya da rikon amana.
Shugaban kwamitin, ya yi godiya bisa yarda da shi da aka yi har aka ba shi wannan aiki, sannan kuma yi yi alkawarin cewa zai yi aiki mai kyau.
Kamfanin Dillancin Najeriya ta ruwaito cewa an ba kwamitin kwana 10 ne domin kammalawa tare da hada rahotonsa.