Rundunar sojin Najeriya ta bayar da sanarwar cewa ta canja mai magana da yawunta , inda ta maye gurbin birgediya janar Sani Usman Kukasheka a matsayin mai magana da yawunta din da birgediya janar Jude Chukwu kamar the Cable ta ruwaito..
A yanzu haka Kukasheka yana karatu ne a makarantar manyan jami’an gwamnati NIPS da ke Kuru a garin Jos na Jihar Filato.