✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rundunar sintiri ta kama barayin wayoyin lantarki a Kano

Za mu kamo ragowar masu laifin domin gurfanar da su a Kotu.

Rundunar sintiri ta jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC), ta kama barayin wayar lantarki a Karamar Hukumar Kura da ke Jihar Kano.

Kwamandan rundunar a Kano, Adamu Idris Zakari ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a birnin Dabo.

Ya ce, kamen ya biyo bayan tattara bayanan sirri da korafi da suka samu daga mahukuntan Babban Asibitin Kura game da sace-sacen kayan wutar lantarki a yankin.

Dauri-dauri na wayoyin lantarki da barayin suka sata

Bayanai sun ce, sakamakon wannan ce, rundunar ta samu nasarar kama wasu matasa biyu – Surajo Tanimu da Ghali Ali – da dauri-dauri na wayoyin lantarki samfurin ‘Armo’ mai kimanin tsahon mita 8 wanda darajarta ya kai kimanin naira miliyan daya.

Kazalika, Zakari ya bayyana cewa, jami’an sintirin sun samu nasarar kwato wata wayar lantarki mai karfin 32KVA a wani sumame da suka kai a Karamar Hukumar Gaya a jihar.

Ya ce, barayin wayar sun yasar da ita a gefen hanya a yayin da suka fahimci jami’an sintirin na daf da kama su.

“Mun fara bincike, kuma muna masu tabbatarwa da al’umma za mu samo wadannan masu laifi domin gurfanar da su a Kotu, a cewar Kwamanda Zakari.