Rundunar sintiri ta jami’an Hukumar Sibil Difens (NSCDC), ta kama barayin wayar lantarki a Karamar Hukumar Kura da ke Jihar Kano.
Kwamandan rundunar a Kano, Adamu Idris Zakari ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a birnin Dabo.
Ya ce, kamen ya biyo bayan tattara bayanan sirri da korafi da suka samu daga mahukuntan Babban Asibitin Kura game da sace-sacen kayan wutar lantarki a yankin.
Bayanai sun ce, sakamakon wannan ce, rundunar ta samu nasarar kama wasu matasa biyu – Surajo Tanimu da Ghali Ali – da dauri-dauri na wayoyin lantarki samfurin ‘Armo’ mai kimanin tsahon mita 8 wanda darajarta ya kai kimanin naira miliyan daya.
Kazalika, Zakari ya bayyana cewa, jami’an sintirin sun samu nasarar kwato wata wayar lantarki mai karfin 32KVA a wani sumame da suka kai a Karamar Hukumar Gaya a jihar.
Ya ce, barayin wayar sun yasar da ita a gefen hanya a yayin da suka fahimci jami’an sintirin na daf da kama su.
“Mun fara bincike, kuma muna masu tabbatarwa da al’umma za mu samo wadannan masu laifi domin gurfanar da su a Kotu, a cewar Kwamanda Zakari.