A farfajiyar Ifiriki
An afka rukuki
Ana amsa sallamar ma-ki baki
An niki gari niki-niki
Ana nuna kiyayya cikin lakaki
A kadadar kudun karantar yabanya
An samu tawaya
An yi rububin rufe tukunya
An ga kowa yai turjiya
An zo ana faman neman yafiya
Ba wata togaciya
An san masu kafiya
Da masu jimirin juriya
Jigari-jigarin jirgiya
Jan jama’ar jerangiya
Fito-na-fito ba kwankwatsa
An dai yaga cunar hantsa
Ga cizon kunama an gartsa
Ana ta nunin yatsa
Irin fitinar Peter Botsa
Bankaurar bakin Baturen bukkar babbake baki
Ba baren baki-baki
Balullubar bugi-in-bugar bakake
Ba wanda ya san an wasa wukake
Bahallatsar birgimar bijiro da tarnaki
An dai yi fashe-fashe
Dukiya an wawushe
Wai haushi aka huce
Lakumar rayuka kamar hoce
Aka karke da kashe-kashe
Zaman gidan-Buwai
Zuwan Baban bawai
Zancen ai-ai
Zambar wai-wai
Ziyarar kawai-kawai
Garbatin garbai
Kwanaren kwashe-kwashen kwabbai
Motsin muttsuttsuke matsabbai
Birkice-birkicen baibai
Tamoji-tamojin tabe tabbai
Ifiriki
Na da dan ‘uwa mummuki
Mariki
Mai dan maraki
Ba ya bankar buki
Agajinsa har a cikin rukuki
Toye-toyen tawayar tawayen taki
Tunkarar tare tarnaki
Gaba-da-gaban gabagadin garnakaki
Sasarin sarkakiyar sunkurun saki
Sammacen samamen samun saukii
An yi rufa-rufa
An suturta jiki da tufa
Ga tagiya an kafa
Har an sa kafa
Sai kura ta lafa
Rumfar-fansa
Ramar-Faransa
Romon-farin-sa
Ramuwar-fursa
Rarumar fuskar rukurkusa
Rahoton raraka ragas
Ragargaza rukukus
Rankwafawa rakakas
Rafke-rafken rafkiya reras
Rugumniyar rigima rigis
Caccakar cikas
Casawar casa cas-cas
Cukwu-cukwu cus-cus
Karafkiyar karyar karas
Kululun kulle-kullen kus-kus
Canjaras
Carar ci-maka cus
Cake-caken cikas
Cunkushe-cunkushen cushewa cunkus
Cuku-cukun camamar cin ca’ammas
Sasarin sulallan salansa sil
Salular sulalewa subul
Sabin sassabar sollewa sol
Sululun sullutu sul
Sabalikitan solobiyon silili sal
Tsatsubar tsirin tsitakar tsageru
Tsarin tsikarar tsingaro
Tsokale-tsokalen tsananin tsoro
Tsiri-tsirin tsiro
Tsautsayin tsayuwar tsuru-tsuru
Tsaurin tsiya-tsiya
Tsirarun tsaka-mai-wuya
Tsantsame tsamen tsamiya
Tsurkun tsukukun tsakar tsargiya
Tsororuwar tsagwaron tsikarar tsintsiya
Karon-battar kudancin Ifrikiyya
Karo-da-karon kakarin kariya
Kandamar kunun kwalfiya
Kafa kantunan kurda-kurdar kurdiya
Kashe fatarin faharin tsiya
Kasashe na ginuwa ne da baki
Akwai farare da bakake
Kuna ta noke-noke
Kun karke da duke-duke
Ba kwa kishin Ifiriki
Bakan-gizo
Bakar alewa tai gizo
Bugun buguzum da hazo
Buzuzu bazo-bazo
Bako da bakuwa sun zo
An ga tozo
An yi aringizo
Ana ta kwarmaton kwakwazo
Anai wa mutane kozo
An dai gaza samun gwarzo
Kasa mai sasarin wariya
Hargagin harin ’yan Haurobiya
Jimurdar ja-in-jar jirgiya
Bakin birgimar baudiya
buji-bujin bulaliya
Mamayar mutane
Mahaifar Maman-tine
Makarkashiyar mirgine-mirgine
Madubin Madibar mintsine- mintsine
Mui masalaha mu manne
Shagon shafin-rata
Rugumutsin kaya ratata
Kun bararraje kun sakata
Bakan-kizo ko ba bukata
Rayuwa babbar makaranta
Bakin satar biki
Asusun sautun baki
Dukiyar darkaki
Ku tattare kui daki
Kun samar wa kasarku taki
Kuna kukan mamayar bakinku ne
Yawan cinikin kayan mayen masu sane
Keta haddin adon-gari a kwane-kwane
Kisa da wawushe dukiyar bakin zaune
Azargagiyar zargin wanne ne
Dambarwar dukunkune-dukunkune
Karami-karami kankane-kankane
Kasurar kundunbalar karfafa kone-kone
Kasa da kasa na ta gane-gane
Damben dabarbarun danne-danne
Jita-jitar jigata
Jagwalgwalon jangwalota
Jimurdar jimami jim
Jijjiga jugum-jugum
Ja-in-jar jajen juyin jarabta
Zomon zamiyar zama
Zugar zirga-zirgar Zangina
Ziryar zabarin zanga-zangar lumana
Zumun zamanin zakwadin zuma
Zakin zukar zuki-ta-mallen zalama
Mu dubi Manin-Dela
Mutumin da yai fafutikar hana lalala
Mai karsashin kassara kasala
Ya shiga sasarin yarin wahala
Haurobiya ta nuna kula
Dabaibayin dagar Desmond Tutu
Yai fama da masu kutu-kutu
Da dimbin mabiyansa rututu
Haka ya fafata ba hutu
Yai ta isar da sakonnin sautu
Babban baban zulu
Yai hani da sharholiyar hululu
Kada dararraku su zam kukan kululu
Matukar akai ta farfasa tulu
Hanin makwalwar modar baki sai butulu
Gwanintar guje wa gardamar garada
Ga gada-gadar gudun gada
Don gudun ta’adar tada kan adda
Ko jawo hadurran kasada
Wai baudaddu ne barada
Wadanda suka ki ji
Tuni sun afka daji
Sun gaza tayar da kwanji
Sai kukan kaji
Ana ta fama da kumburin kurji
Masu mugun nufi
Sun daba wa cikinsu tsitakar kaifi
Sai ta huda kurungu mai shafi
Kui nazarin littafi shafi-shafi
Ko kun zama masu gyaran ta’asar laifi
A rika bai wa juna tallafi
A kauce wa tsatsubar tsafi
Kyawawan ta’adu ai musu kafi
Miyagun ta’adu a magance nasu dafi
Rufin asirin suturta juna da tufafi
Sha’anin shugabanci
Shugaba ya zam mai adalci
Al’ummar kasa a kiyayi butulci
Mu zam masu mutunci
Da ke fafutikar yaye duhun jahilci
Mu yasar da ta’adar wawanci
Da dallakin dalalar dolanci
Ko kwabar kwafsawar batanci
Ka da a shiga kunci
Tattare da kaskanci
Haurobiyawa
Ban da ramuwar gayya
Ku nusar da kyawun halayya
A wajen neman halaliya
Babu duk wata kokowa
Ba gyare-gyare
Irin na kurege da gyare
Ko kankare kure
Da aikin kuskure
Kowane Ifiriki a zam ba bare
A daina bore
Mu kyautata zaman tare
Hawayen kowa a share
Mu samu mu murmure
Kar mu biye wa ’yan ta-more
Kowa ya hadiye haushi
A bar fusatar fushi
Ko fafata farmakin fashi
Basajen basarwar bushi
Kar a zo ana bashi-bashi
Shaidancin shure-shure
Sasarin sare-sare
Turka-turkar takura ta tokare
Taratsin tunkara ta tubure
Ta’adar tarairaya ta tabarbare
Tereren turereniya
Tunkude-tunkude tukunya
Tafarfasar turka-turkar turjiya
Takun-sakar sarkakiy
Tunkunyin tunkun tankiya
Mui ta’awuzi
Mui nema daga kanzi
Tare da neman hirzi
A fadar Butar-lazi
Zayyanarmu ta zanu zi-zi
Masu himma
Magabata sun yi fama
Lallai mui kama-kama
Kowa ya shigo a dama
Amma ban da dama-dama
Mui aiki nagari
Kar a jefa jama’a garari
’Yan kwnatiragin kwagiri
Kui ta kinkimi gatari
Ku zam gatan mazaunan gari
Tarayyar Ifrikiyya
Ai gangamin gayyatar gamayya
Ai kokarin dakushe dafin kiyayya
Ai ta nuna sanayya
Turmutsitsin taron tallafin tarayya