✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rukunin farko na maniyyatan Kano sun tashi zuwa kasa mai tsarki

Maniyyatan su 555 sun tashi a cikin jirgin Max Air

A ranar Litinin rukunin farko na alhazan Jihar Kano su 555 sun tashi zuwa kasa mai tsarki.

Maniyyatan sun tashi daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano da tsakar rana a jirgin kamfanin Max Air kirar Boeing 747.

Ana sa ran alhazan wadanda suka fito daga Kananan Hukumomin Doguwa da Tudun wada da Bebeji da Garun Malam za su sauka a Madina.

Yayin da yake jawabin a wajen, Gwamnan Jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnati ta yi duk mai yiyuwa wajen ganin an samar wa da alhazan abubuwan da suke bukata a kasa mai tsarki

Ya kuma bukace su da su zama jakadan Jihar nagari a kasa mai tsarki ta hanyar nuna halaye nagari da da’a yayin zamansu a can.

“Muna jan kunnen maniyyatanmu da su kasance jakadu nagari kasa mai tsarki kada su shiga cikin duk wasu ayyuka na rashin kirki kamar su fataucin miyagun kwayoyi da sata da zanga-zanga da sauransu”.

Da yake jawabi tun da farko, Darakta Janar na Hukumar Jin dadin Alhazan Jihar, Alhaji Lamin Danbappa, ya bayyana cewa maniyyatan da za su tashi a yau din su ne wadanda ba su sami tafiya kasa mai tsarki ba saboda sakaci na gamnatin da ta gabata.

“Wadannan su ne alhazan da ba su sami tafiya Aikin Hajji a bara ba saboda rashin mayar da hankali na gwamnatin da ta gabata. Shi ya sa a bana muka fara da su don mu kyautata musu,” in ji shi.

Shi ma da yake jawabi, jami’in kamfanin sufurin jiragen sama na Max Air, Alhaji Abdullahi Bawa, ya bayar da tabbacin yin jigilar alhazan a kan lokaci.

“A shirye muke mu ci gaba da gudanar da jigilar alhazan akan lokaci. Ko a yau idan Hukumar Alhazan ta shirya za mu iya kawo jirgi don kwashe wasu alhazan zuwa kasa mai tsarki”.

Auwalu Danladi Garun Malam daya ne daga cikin maniyyatan, ya gode wa Gwamnatin Jihar bisa gyara da ta fara yi a sansanin alhazan Jihar.