A kofar shiga wata jami’a a kasar Afirka ta Kudu an rubuta wani sako kamar haka: “Ruguza kowace kasa ba ya bukatar sai an yi amfani da bama-bamai ko makamai masu linzami, abin da ake bukata kawai shi ne a rage darajar ilimin kasar ta hanyar kyale dalibai su rika satar jarrabawa.” Saboda haka masana sun bayyana cewa:
– Idan haka ta faru, marasa lafiya za su rika mutuwa a hannun likitocin wannan kasa.
-Gine-gine za su rika rushewa a hannun injiniyoyin wannan kasa.
-Kudi za su rika bacewa a hannun akantoci da masana harkokin tattalin arziki da ke kasar.
– Za a rasa tausayi da tawali’u a tsakanin malaman addini na wannan kasa.
– Za a rasa adalci a wurin lauyoyi da alkalan wannan kasa.
– Za a rasa jagoranci nagari daga wurin ’yan majalisar wannan kasa.
– Idan wadannan abubuwa suka faru, kasa ta gama rugujewa.
Yanzu a Najeriya satar jarrabawa ta zama ado, ba a ko jin kunyar aikata ta, hasali ma dai iyayen yara da malamansu ne da kansu suke taimakawa wajen satar jarrabawa. Domin har kudi suke ba malamai domin su taimaka wa ’ya’yansu su ci jarrabawa.
Akwai makarantun da suka yi suna wurin magudin jarrabawa, matukar iyayen yara sun yi wa ’ya’yansu rajistar jarrabawa a wadannan makarantu, to, babu shakka ’ya’yansu za su ci jarrabawar, domin kudin da za su biya na jarrabawar daban ne da na sauran makarantun da ba a yin magudi. Shi ya sanya ake samun dalibi zai yi karatu a wata makaranta amma idan an zo rubuta jarrabawar karshe ba zai rubuta a makarantar ba, sai ya koma wata ya rubuta saboda a can ne yake da tabbacin zai ci jarrabawar, saboda ya biya kudi mai yawa.
Haka za a ci gaba da magudi a karatun har zuwa jami’a, ana ta karatun zuku har a fita daga jami’ar a je a kama aiki da sakamako mai kyau a kwali kawai, amma mai wannan sakamako ba zai iya kare sakamakon da ya samu a aikace ba.
Wannan yana faruwa ne saboda fiffikon da ake ba kyakkyawan sakamako a rubuce maimakon mayar da hankali a kan aiki a aikace. Shi ya sanya ake ta kokarin mallakar takardar sakamakon karatu mai kyau ko ta wane irin hali.
Idan dalibi ya mayar da hankali wajen yin karatu tsakani da Allah, idan bai yi sa’a ba, malamin nasa sai ya kayar da shi, saboda idan mace ce ta ki biya masa wata bukata tasa, idan kuma namiji ne saboda wani abu da ya shiga tsakaninsu. Idan kuma har sun yi sa’a sun tsallake to makin da za su samu ba zai kai na wadanda suka bayar da kai bori ya hau ba.
Shi ya sanya yanzu bara-gurbin dalibai suka mamaye ko’ina a makarantu da sauran wuraren ayyuka.
Ta yaya mutumin da bai iya komai ba zai koyar da wani, me zai koyar in ban da shirme? Idan kuma a sauran wuraren aiki ne, za a dauki mutum da takardar karatu mai kyau, amma duk aikin da aka sanya shi ba zai iya ba.
Ta yaya kasa za ta ci gaba da irin wadannan bara-gurbin mutane?
An dauke su aikin koyarwa amma maimakon su karantar da daliban nasu sai dai su karkatar da su, domin su ma ba su iya ba balle su koyar da wadansu.
Abin tsoron shi ne, nan gaba kadan ilimi zai bace a kasar nan saboda jahilai ne za su zama jagorori a fagen ilimi.
A baya wanda ya yi karatun firamare ya fi wanda ya yi karatun sakandare a yanzu, wanda ya yi karatun sakandare ya fi wanda ya yi karatun jami’a a yanzu.
Shugabannin da ya kamata su taimaka wajen gyarawa sai suka koma suna taimakawa wajen lalata al’amura, domin su ma suna kai ’ya’yansu makarantun da ake kashe kudi ana samun sakamako mai kyau ne, a cikin gida Najeriya ko a kasar waje. Yanzu ma sun fi tura ’ya’yansu kasashen waje su yi karatu saboda sun tabbatar makarantun Najeriya ba su da inganci. Alhali mafi yawansu irin wadannan makarantu da suke gudu suka yi, amma suka bari suka lalace, sai talakawa da ya zama musu dole ne suke tura ’ya’yansu saboda babu yadda za su yi.
Ya kamata shugabanni su fahimci cewa ilimantar da ’ya’yansu su bar na talakawa ba dabara ba ce, domin wadannan yaran da aka hana su ilimi mai inganci ba za su bar ’ya’yan nasu su zauna lafiya ba.
Haka kuma duk da kashe makudan kudaden da suke yi ba dole ne ’ya’yan nasu su yi karatun ba, saboda shagwaba yara da suke yi sai su je makarantar su kara lalacewa saboda haduwa da wadansu ’yan gata marasa tarbiyya da suka yi a makarantar.
Saboda haka ba a yi wa Allah wayo, ko dai shugabanni su yi abin da ya kamata wajen samar da ilimi mai inganci ga kowa, ko kuma su koma suna nadamar abin da suka aikata a lokacin da nadamar ba ta da amfani. Inganta harkar ilimi, inganta kasa ce. Akasin haka kuma kashe kasa ce, domin ba a iya rike kasa da jahilci.