Shugaban Jami’ar Benin da ke Jihar Edo, Farfesa Lilian Salami ya ce wasu daga cikin daliban makarantar sun fara aikewa da sakonnin barazanar dukan malansu matukar aka ci gaba da rufe jami’o’in gwamnati.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa a cikin shirin Good Morning Nigeria na gidan talabijin na NTA ranar Laraba.
- Jami’ar ABU Zariya ta sanar da ranar komawar dalibai
- Ma’aikatan jami’o’in Najeriya za su shiga yajin aikin sai Baba ta gani
Daliban jami’o’in gwamnati a Najeriya dai sun fara zaman gida ne tun a watan Maris na shekarar 2020 lokacin da Kungiyar Malaman Jami’a ta Kasa (ASUU) ta fara yajin aiki wata tara saboda kin biya bukatun ’ya’yanta.
Sai dai a ranar 24 ga watan Disamba kungiyar ta sanar da janye yajin aikin bayan kai ruwa rana da gwamnati.
Duk da haka, murnar daliban ta ci gaba da karatu ta sake komawa ciki sakamakon sake barkewar annobar COVID-19 a karo na biyu, lamarin da ya tilasta sake rufe makarantun har zuwa 18 ga watan Janairun 2021.
A bangare guda kuma sauran kungiyoyin ma’aikatan jami’a na barazanar shiga yajin aiki saboda rikici kan kudaden da gwamnati ta bayar domin biyan bukatun jami’o’in,
Shugaban jami’ar ya ce lamarin ya jawo wasu dalibai sun fara barazanar dukan shi da ma sauran malaman makarantar.
“A zahirin gaskiya, na ma ji wasu dalibanmu suna cewa idan ba mu bude makarantu ba, za su doke ni da ma sauran malaman makarantar.
“Watakila wasu shugabannin jami’o’in za su iya jure duka, amma Farfesa Lilian ba zai iya jurewa ba.
“Za mu yi iyakar kokarinmu wajen ganin mun kare dalibai, malamai da sauran ma’aikata daga wannan cutar da zarar an bude makarantu.
“Jami’armu ta fara sarrafawa tare da samar da kayayyakin tsaftacewa da wanke hannu da ma sauran kayayyaki masu muhimmanci wajen yaki da cutar,” inji Farfesa Lilian.
Idan za a iya tunawa, ko a cikin makon nan sai da ASUU ta yi gargadin cewa akwai hatsari a sake bude jami’o’i saboda karancin matakan kariya da za su tabbatar da bayar da tazara a azuzuwa da dakunan kwanan dalibai.