Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta soki lamirin matakin da wasu Gwamnonin yankin suka dauka na rufe kasuwanni da makarantu da kuma hana zirga-zirga da cinikin dabbobi a matsayin hanyar dakile kalubalen tsaro.
A cikin makon nan ne dai Hukumar da ke Kula da Kafafen Sadarwa ta NCC ta ba da umarnin rufe hanyoyin sadarwa a Jihar Zamfara saboda karuwar kai hare-hare da satar dalibai.
- Sojoji sun yi juyin mulki a kasar Guinea, sun tsare Shugaban Kasa
- An sace mata da ’ya’yan dan majalisar Katsina
Kazalika, wasu Jihohi kamar Kaduna da Neja su ma sun dakatar da cin kasuwannin mako-mako da takaita sayar da man fetur a jarkoki a cikinsu.
Sai dai kungiyar dattawan, ta bakin kakakinta, Dokta Hakeem Baba-Ahmed a cikin wata sanarwa ranar Lahadi ta ce matakan kawai kara karfafa gwiwar ’yan bindigar za su yi a maimakon dakile su.
Baba-Ahmed ya ce matakan wasu hanyoyi ne na kakaba wa tattalin arziki da walwalar jama’a sabuwar dokar kulle, duk da cewa sun jima suna kwasar kashinsu a hannun ’yan bindigar.
Ya ce matukar ba a dauki kwakkwaran mataki a kan ’yan bindiga da masu satar mutane ba, matakan za su kara wa jama’a halin kuncin da suke ciki ne.
“Abu mafi muni kuma shi ne za su kara samun kwarin gwiwa musamman in suka fahimci babu wani abu da gwamnati za ta iya tsinana wa ban da kulle jama’a.
“Su kansu mutanen da abin ya shafa za su yanke kauna daga gwamnati kan kare su.
“Batun cewa mutane su za su kare kansu ba abu ba ne mai kyau, amma dole hakan ce za ta kasance idan suka fahimci cewa bata-gari na cin karensu ba babbaka,” inji Dokta Baba-Ahmed.
Daga nan sai kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da na Jihohi da su kawo wa yankunan da suke cikin halin ni-’ya-su dauki.