Shugaba Muhammadu Buhari ya ce rufe iyakokin Najeriya na kan tudu bai hana masu fasakwauri shigo da makamai cikin kasar ta iyakokin ba.
Buhari ya ce rikicin kasar Libya zai jima yana addabar yankin Sahel, muddin tsoffin mayakan da tsohon Shugaba Mu’ammar Ghaddafi ya dauka daga kasashe na rike da makaman da suka sace.
- Aisha Buhari ta dawo Najeriya bayan wata shida a Dubai
- Majalisar Malamai ta nemi Ganduje ya cire wa Abduljabbar takunkumi
- Ba sace ni aka yi ba, guduwa na yi – Amaryar Kano
Ya bayyana hakan ne yayin ganawar bankwana da Wakilin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya a Yammacin Afirka mai barin gado, Mohammed Ibn Chambas a Abuja ranar Alhamis.
Buhari ya ce gwamnatin marigayi Ghaddafi ta samu karfi a shekara 42 na mulkinsa da mayakan wadanda bayan kashe shi suka koma amfani da makamansu suna tayar da zaune tsaye a yankin Sahel.
“Ba abin da suka fi sani kamar su yi harbi su kashe rai, kuma yanzu su ne babbar matsalar yankin Sahel.
“Mun rufe iyakokinmu na kan tudu tsawon fiye da shekara daya amma an ci gaba da fasakwaurin makamai. Muddin ba a samu zaman lafiya a Libya ba, to da sauran rina a kaba.
“Dole mu mike mu magance matsalar, ba za mu yi kasa a gwiwa ba; Daga karshe dai za mu yi nasara,” inji Buhari.
Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da kakakinsa, Femi Adesina ya fitar bayan ganawar tasu da Mista Chambas, wanda ya jima yana aiki a Najeriya a matsayi daban-daban.
Buhari ya yi fatar alheri gare Mista Chambas, wanda shi kuma ya yi godiya game da gudunmuwa da hadin kai da ya samu daga Najeriya da Shugaban Kasar, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa Najeriya za ta ci gaba da zama jagora a Afirka.
Ya ce a bangaren yaki da ta’addanci da tsattsauran ra’ayi Najeriya na taka muhimmiyar rawa musamman wajen taimakon Rundunar Hadin Gwiwar Kasashen Sahel ta MNJTF.