✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rubuta littafi a gidan yari cike yake da kalubale – Fursuna Moshood

Aminiya ta samu tattaunawa da wani fursuna wanda ya shafe shekaru 24 a tsare a gidan yarin kirikiri da ke Jihar Legas mai suna Oladipupo…

Aminiya ta samu tattaunawa da wani fursuna wanda ya shafe shekaru 24 a tsare a gidan yarin kirikiri da ke Jihar Legas mai suna Oladipupo Folaremilekun Moshood. Fursunan wanda tsohon soja ne da aka yanke masa hukuncin kisa daga baya aka mayar da shi daurin rai-da-rai ya zama hamshakin marubuci inda ya rubuta littattafai daban-daban. Moshood wanda yake digirinsa na biyu a halin yanzu a fannin zaman lafiya da sasanta rikici a jami’ar karatu daga gida ta Najeriya, ya yi bayani dalla-dalla yadda ya tsunduma cikin harkar rubuce-rubuce da kalubalen da yake fuskanta. Ga yadda hirar ta kasance:

Ko za ka gabatar da kanka a takaice?

Sunana Oladipupo Folarimilekun Moshood. An haife ni a garin Ibadan da ke jihar Oyo. Yau ina da shekara 62 a duniya. Na yi makarantar firamare da sakandire a garin Ibadan. Daga bisani sai na shiga aikin soja har na kai mukamin kofur. Ina da mata daya da ’ya’ya shida.

Me ya ba ka sha’awa ka shiga harkar rubuce-rubuce?
Gaskiya ni a da ba ni da sha’awar karatu balle ma rubutu. Kuma tun lokacin da na shiga aikin soja ba na tunanin zan koma makaranta na kara ilimi balantana na rika rubuta littafi sai da mai faruwa ta faru. Aka kawo ni nan gidan yari kan zargin yin fashi da makami. Aka yanke mani hukuncin kisa daga bisani aka mayar da shi hukuncin daurin rai-da-rai. A lokacin da na shigo kurkuku sai na yi tunani me zan yi don na inganta rayuwata. Sai na ga babu abin da ya fi ilimi muhimmanci. Saboda haka sai na koma makaranta. Daga bisani kuma sai na fara sha’awar rubuce-rubuce. Saboda ita ce hanya mafi sauki da za ka isar da sako ga jama’a ba tare da wata matsala ba. Ta hanyar rubutu za ka ilimantar da nishadantar kuma ka nusar da jama’a kan wani batu da ba su san shi ba tare da nuna musu illa ko kyawun wani abu.

Littafai nawa ka rubuta kawo yanzu da kake tsare a gidan yari?
Na rubuta littafai da dama wasu an buga su wasu kuma ba a buga su ba. Na fara rubuta littafi na farko mai suna Application of the Rule of Law In Nigerian Political System (Yadda ake amfani da doka a siyasar Najeriya), sai littafin da na rubuta mai suna How Allah Saw Me Through (Yadda Ubangji Allah Ya Cece Ni) da kuma littafin da na rubuta mai suna My Prison Edprience (Rayuwata a gidan yari) da sauran littafai da a yanzu nake rubutawa kan lamarin addini da rayuwa.

Daga cikin littafan da ka ambata wane littafi ne ya fi kwanta maka a rai?
Gaskiya littafin da ya fi kwanta mani a rai shi ne wanda na rubuta a kan yadda ake yin amfani da doka a siyasar Najeriya. Ko kuma yadda ake siyasantar da doka a Najeriya. Ka san shi littafi ne da na rubuta a lokacin da na kammala digiri dina na farko a jami’ar karatu daga gida da ke Jihar Legas. Kuma dalilin da ya sa na rubuta littafin shi ne yadda na ga alkalai da lauyoyi suke murda dokoki bisa son ransu. Wato mutum zai yi laifi amma sai a murda doka a ce bai yi laifin komai ba. Ko kuma mutum ba shi ya yi laifin ba amma kiri-kiri sai a ce ya yi laifi. Kuma fa sun san bai yi laifin ba. To shi ya sa da muka zo karshen karatunmu na digirin farko sai na yanke shawarar na rubuta littafi kan batun. Kuma na yi hira da fursunoni da yawa na ji ta bakinsu. Daga nan sai littafin da na sa masa suna Yadda Allah Ya Cece Ni. Shi ma littafi ne da na rubuta shi kan yadda na tsallake kisa a lokacin da aka yanke mani hukuncin kisa. Allah Ya kaddara ba za a kashe ni ba har daga bisani aka mayar da kisan ya koma rayuwar rai-da-rai a gidan kaso. Sai kuma littafin Rayuwata a gidan yari, (My Prison Edperience). Shi ma littafi ne da na rubuta kan rayuwar da nake yi a gidan yari. Yadda muke rayuwa da abubuwa masu tayar da hankali da tausayi da na farin cikin da na bakin ciki da ibada da sauransu da muke yi a cikin gidan yari.

Wane kalubake kake fuskanta a harkar rubuce-rubucen da kake a gidan yari?
Akwai kalubale da iri-iri masu yawan gaske. Na farko dai akwai kalubalen karancin kudi. Sau da yawa idan ka rubuta littafi, kudin da za ka buga shi wani tashin hankali ne. Tun da kana fama da abin da za ka ci balantana kudin buga littafi, sannan kuma yadda za ka samu wanda zai rika kai maka rubutun naka waje ana gyarawa da kuma yadda za ka samu madaba’ar da za ta buga maka littafin. Galibi mun dogara ne da jami’an gidan fursuna da wasu kungiyiyo da suke shigowa suna kawo mana ziyara. Su ne suke tallafa mani. Akwai kungiyar da ta ba ni kudi na buga littafi. Sannan kuma akan samu daidaikun mutane da muke zaune da su a cikin gidan yari da Allah Ya hore musu abin duniya, su ma suna tallafa mani da kudi da duk abin da na nema. kalubale na biyu shi ne samun kwanciyar hankalin da za ka yi rubutun. Don shi zaman gidan yari zama ne na zullumi da tashin hankali. Idan kana cikin ka yi ta sake-saken abubuwa iri-iri. Tun ba ma a ce an yanke maka hukuncin kisa ba, kullum tunaninka mutuwa. A yanzu haka akwai littattafan da nake so na buga su na fitar da su kasuwa amma rashin kudi shi ne yake kawo mani cikas. Kodayake ni ba damuwa na yi na ci wata riba ba.

Wane buri kake so ka cinmawa a rubuce-rubucen da kake yi?
To ni burin da nake so na cin mawa shi ne, ya zamana littattafaina sun samu karbuwa ga jama’a, ya zama sun amfana sun sami ilimi mai yawa ta hanyar littattafaina. Kuma ina da burin idan Allah Ya yi mani tsawon rayuwa in ci gaba da karatu har matakin Farfesa kuma in ci gaba da rubuta littafai har karshen rayuwata.