Rahotanni daga birnin Paris na cewa tsohon kocin Real Madrid, Zinedine Zidane na shirin kulla yarjejeniya da Cristiano Ronaldo na Manchester United zuwa kungiyar Paris Saint-Germain.
Jaridar Daily Mirror da ke Birtaniya ta ruwaito cewar Zidane na gab da komawa PSG a karshen kakar wasa ta bana, wanda kuma bukatarsa ta farko ita ce kungiyar ta bashi damar kawo Ronaldo gasar Ligue 1 ta Faransa.
- Tsuguno bata kare ba: Salah ya samu damar daukar fansa a kan Mane
- Ronaldo ya zama mutum na farko da ya samu mabiya miliyan 400 a Instagram
Rahoton jaridar Marca da ke Sifaniya ya kara da cewa ana sa ran Ronaldo mai shekaru 37 zai gaggauta karbar tayin Zidane don kafa tarihin buga wasa tare da Lionel Messi da Neymar a PSG.
Ana sa ran Zidane zai maye gurbin kocin PSG na yanzu, Mauricio Pochettino, wanda ake alakanta shi da komawa Manchester United don maye gurbin Ralf Rangnick a karshen kakar wasa ta bana.
Har yanzu dai akwai kyakkyawar alaka tsakanin Zidane da kuma Ronaldo tun bayan zaman aikin da suka yi tare a Real Madrid, inda tare suka lashe kofin gasar zakarun Turai sau uku a jere.
Tuni dai PSG ta yi kokarin kulla yarjejeniya da Ronaldo a baya, amma ta kasa shawo kan kyaftin din na kasar Portugal don ya koma Faransa.
PSG ta tuntubi Zidane don maye gurbin Pochettino
Tun a watan Nuwambar bara Kungiyar PSG ta soma tuntubar Zinedine Zidane mai shekaru 49 domin kulla yarjejeniya da shi a matsayin sabon kocinta.
Bayanai sun ce Zidane da wakilan PSG sun yi ganawar farko ne a Royal Monceau daya daga cikin otal-otal mafi girma a birnin Paris.
Jaridar Le Parisien ta ruwaito cewa daga cikin wadanda suka gana da Zidane akwai daraktan wasannin PSG Leonardo da kuma Jean-Claude Blanc, babban manajan kungiyar wanda kuma amini ne ga Zidane.
Wannan tattaunawa dai ta jefa makomar kocin PSG na yanzu Mauricio Pochettino cikin hali na rashin tabbas, wanda tuni ya soma fuskantar suka kan rashin tabuka abin kirki a gasar zakarun Turai a wannan kakar, musamman ma a wasan da suka buga da Manchester City, wadda ta lallasa su da 2-1 a gasar Kofin Zakarun Turai.