Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Manchester Uniter, Cristiano Ronaldo ya kafa tarihin zama mutum na farko da ya taba samun mabiya miliyan 400 a shafin sada zumunta na Instagram.
Dan wasan da ya cika shekara 37 a duniya a ranar Asabar, ya fara samun mabiya miliyan 200 a shafin na Instagram ne a 2020.
- Guguwar Batsirai ta hallaka gommai a Madagascar
- Rikicin APC a Kano: Za a yi ‘raba-daidai’ tsakanin tsagin Ganduje da na Shekarau
Sai dai cikin shekara guda mabiyan, nasa sun kara rubanya har sau biyu.
Yawancin abin da Ronaldo ke wallafawa a shafin nasa bai wuce abin da ya shafi iyalansa, harkar kwallon kafa da kuma abin da ya shafi kamfaninsa na CR7 ba.
Dan wasan wanda dan asalain kasar Portugal ne, shafinsa ne na biyu wanda ya fi na kowa samun adadi mafi yawa na mabiya baya ga shafin Instagram, mai mabiya miliyan 469.
Shafin na Instagram ya wallafa bayanai 6,600 wanda suka shafi sabbin bayanai da dokokin da suka jibanci amfani da shafin na sada zumunta.