Cristiano Ronaldo ya sha gaban Pele wurin zira kwallaye a raga, inda ya zamo dan kwallo na biyu mafi zira kwallaye a tarihin tamaula.
Fitaccen dan wasan ya cimma wannan mataki ne a wasan da kungiyarsa ta Juventus ta kara da Udinese a gasar Serie A wanda aka tashi 4-1 a ranar Lahadi.
- ’Yan ta’adda sun yi wa mafarauci yankan rago a Abuja
- Coronavirus ta kashe mutum 9 a Najeriya, 917 sun kamu
- Bayan shekaru 15 Bafarawa ya kai ziyara gidan Wamakko
Dan wasan gaban na Kasar Portugal ya jefa kwallaye biyu a wasan cikon ta 757 da 758 a tarihinsa na kwallo mai cike da ban mamaki da kuma kayatarwa.
Alkaluma sun nuna cewa Pele ya jefa kwallaye 757 a tarihinsa na kwallo a kungiyar Santos da New York Cosmos da kuma Kasarsa ta Brazil a tsakanin shekarar 1956 zuwa 1977, sai dai a yanzu Ronaldo ya turo shi mataki na uku a jerin ’yan kwallo mafi zira kwallaye bayan da ya jefa kwallonsa cikon ta 758.
A halin yanzu dai, Josef Bican shi ne dan wasa mafi zira kwallaye a tarihi wanda ya ci kwallaye 759 daga shekarar 1930 zuwa 1950 a kungiyoyin Slavia Prague da FC Vitkovice da Rapid Vienna da Admira da FC Hradec Kralove.
Hakan na nufin saura kwallo daya tilo kenan Ronaldo ya kamo Josef Bican a matsayin dan wasa mafi zira kwallaye a tarihi.
Ronaldo yana da damar kamo Bican har ma ya sha gabansa a yayin da Juventus za ta ziyarci AC Milan a daren Laraba a wani wasa mai muhimmaci da kungiyarsa za ta fito kwanta da kwarkwata don ganin ta kare kambun zakarun Serie A da ke hannunta.