✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya sanya ranar aurensa

Shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid na Sifen dan asalin Fotugal Cristiano Ronaldo a ranar Talatar da ta wuce ne ya ce shi da…

Shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid na Sifen dan asalin Fotugal Cristiano Ronaldo a ranar Talatar da ta wuce ne ya ce shi da budurwarsa Georgina Rodriguez sun sanya lokacin da za su yi aure.

Kamar yadda rahoton ya nuna, yanzu masoyan biyu za su yi aure ne da zarar an kammala Gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a badi idan Allah Ya kaimu.

Ronaldo wanda ya haihu sau uku tare da budurwar tasa kuma yanzu tana dauke da cikinsa na hudu, ya ce da zarar  Fotugal ta samu nasarar lashe kofin kwallon kafa na duniya a badi a Rasha zai sanar da takamaiman ranar da zai angwance da budurwarsa.

Ronaldo wanda yanzu haka shi ke rike da kambun Gwarzon kwallon kafa na Duniya ya ce yana fata kasarsa Fotugal ce za ta lashe kofin a badi a Rasha kuma hakan ne zai ba shi damar yanke takaimaman ranar da zai yi aure.

dan shekara 32, dan kwallon ya ce yana fata kasarsa za ta lashe kofin kwallon kafa na duniya a karon farko a tarihin gasar da hakan zai karfafa masa wajen sanar da ranar aurensa.