✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya samu magoya baya miliyan 100 a facebook

A halin yanzu shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen kuma haifaffen Fotugal Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi na zama dan…

A halin yanzu shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen kuma haifaffen Fotugal Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi na zama dan wasan da ya fara samun masoyan da suka kai miliyan 100 a dandalin sadarwarsa na facebook.

A yanzu za a iya cewa Ronaldo ya zarce Lionel Messi da yawan masoya kimanin miliyan 26 bayan da Messin yake da masoya su kimanin miliyan 74 a kafar sadarwar Facebook.
Wannan adadi da dan kwallon ya samu ta sa ya zarce duk wani dan wasa samun magoya baya a shafin sadarwar facebook a fadin duniya.
Yadda jadawalin ya nuna shi ne Lionel Messi ya kasance yana da masoya miliyan 76 ne yayin da tsohon dan kwallon Manchester United Dabid Beckham yake da masoya miliyan 50 sai Wayne Rooney shi ma da ke kwallo a kulob din Manchester United na Ingila yake da miliyan 25 yayin da Zlatan Ibrahimobic dan kwallon PSG da ke Faransa yake da miliyan 20.
Kazalika Ronaldo ya doke yawan masoya kulob din Real Madrid da na FC Barcelona duk a Sifen a shafin na facebook, bayan kulob din Madrid yana da miliyan 75 yayin da na FC Barcelona kuma yake da miliyan 76.
Tuni Ronaldo ya bayyana farin cikinsa a kan wannan nasara da ya samu inda ya ce bai taba tunanin zai iya samun adadin masoya haka a hsafin sadarwa na facebook a fadin duniya ba.