✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Ronaldo ya rabu da budurwarsa

Rahotanni sun nuna Gwarzon dan kwallon duniya a bana Cristiano Ronaldo ya rabu da budurwasa ’yar asalin Rasha mai suna Irina Shayk bayan ta ki…

Rahotanni sun nuna Gwarzon dan kwallon duniya a bana Cristiano Ronaldo ya rabu da budurwasa ’yar asalin Rasha mai suna Irina Shayk bayan ta ki halartar bikin zagayowar ranar haihuwar mahaifiyarsa mai suna Dolores Abeiro a karshen makon jiya.

Mahaifiyar Ronaldo ta yi bikin cika shekara 60 ne amma duk da ya aika mata katin gayyata ta ki halartar bikin, al’amarin da ya bata masa rai kuma ya yanke shawarar ya rabu da ita.
Haka kuma rahoton da kafar sadarwar UK Mirror ta kalato ta ce budurwar tasa ba ta halarci bikin Gwarzon dan kwallon Duniya da ya gudana a Suwizilan a makon jiya ba, gasar da dan kwallon ne ya samu nasarar lashewa.
Sai dai rahotanni sun tabbatar Miss Irina Shayk, budurwar ta Ronaldo ba ta ga-maciji ga mahaifiyarsa da kuma kannensa mata, al’amarin da ya sa budurwa take baya-baya ga iyalan nasa.
Alamun rabuwa da budurwasa sun tabbata ne a karshen makon jiya a lokacin da dan kwallon yake jawabin godiya jim kadan bayan ya lashe Gwarzon dan kwallon duniya amma bai ambaci sunanta ba sai dai kawai na takwarorinsa na kulob din Real Madrid da na abokai da iyalansa da kuma ’yan uwa.
Ronaldo dai ya dade yana soyayya da Irina Shayk al’amarin da ya sa da dama suka dauka ita zai aura.