✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya raba gari da Manchester United

Muna yi masa fatan alheri da shi da iyalansa.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta cimma yarjejeniyar raba gari da tauraronta dan wasan gabanta, Cristiano Ronaldo nan take.

Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a yammacin Talatar nan, ta ce an cimma yarjejeniyar raba garin ce a tsakanin bangarorin biyu.

“Kungiyar Manchester United tana cike da godiya dangane da gudunmawar da ya bayar a zaman wa’adi biyu da ya yi a Old Trafford.

“Muna mika godiyarmu musamman ga kwallaye 145 da jefa wa kungiyar cikin wasanni 346 da haska mana.

“Muna yi masa fatan alheri da shi da iyalansa.

“A halin da ake ciki kungiyar Manchester United ta mayar da hankalinta wajen ci gaba da aiki tare a matsayin tsintsiya madauri daya karkashin jagorancin Erik ten Hag domin samun nasara,” a cewar sanarwar.