✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon dan wasan watan Fabrairu a Saudiyya

Wasa kadan Ronaldo ya yi wa Al-Nassr, amma har ya zura kwallo takwas.

Cristiano Ronaldo shi ne ya lashe kyautar gwarzon kwallon kafa na watan Fabrairu a Gasar Saudiyya ta Saudi Pro League.

Karon farko da ya karbi kyautar a sabuwar kungiyarsa Al-Nassr, wadda ya koma a watan Janairu daga Manchester United kamar yadda Marca ta wallafa.

Wasa kadan Ronaldo ya yi wa Al-Nassr, amma har ya zura kwallo takwas, yanzu yana da tazarar biyar tsakaninsa da takwaransa Talisca mai 13, wanda shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar.

A wasa biyu baya da ya buga ya sharara kwallo bakwai a raga, sannan ya bayar da biyu aka ci.

Ya kuma fara da cin kwallo a karawar farko da ya fara yi wa Al-Nassr, wadda ya koma da taka leda, bayan kammala Gasar Kofin Duniya.

Haka kuma Vincente Moreno ya lashe kyautar kocin da ba kamarsa a watan Fabrairu a gasar ta Saudi Arabia.

Tsohon kociyan Mallorca da Espanyol, wanda ke horar da Al Shabab, ya lashe kyautar karo na uku kenan.

Wanda ya karbi kyautar mai tsaron raga da yafi taka rawar gani shi ne Marcelo Grohe, mai shekara 36.

Tsohon golan Gremio, wanda ya tsare ragar tawagar Brazil karo biyu, yanzu yana taka leda a Al-Ittihad.

Aminiya ta ruwaito cewa a farkon makon nan ne Lionel Messi ya lashe kyautar gwarzon kwallon kafa na duniya na FIFA na 2022 a bikin da aka gudanar a Faransa.