✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Ronaldo ya ki karbar tallar Pepsi saboda zargin kamfanin wajen taimaka wa Isra’ila

Cristiano Ronaldo wanda ke taka leda a kulob din Real Madrid na kasar Sifen ya ki karbar tallar kamfanin Pepsi saboda zargin da yake yi…

Cristiano Ronaldo wanda ke taka leda a kulob din Real Madrid na kasar Sifen ya ki karbar tallar kamfanin Pepsi saboda zargin da yake yi wa kamfanin wajen taimaka wa Isra’ila kan yaki da Hamas.
Kafar yada labarai ta Newsline 77 ne ta buga labarin a shafinta na intanet.
Kwangilar tallar da dan wasan zai sanya wa hannu za ta samar masa da miliyoyin Dala, amma ya ki saboda a cewarsa kamfanin ya taimaka wa sojojin Isra’ila wajen yakar Hamas.  
A kwanakin baya ne dai dan wasan ya ki musayar riga da dan kasar Isra’ila yayin da kasar Portugal ta buga wasan sada zumunci da Isra’ila, inda ya ce ba zai yi musayar riga da makasa ba, al’amarin da ya jawo cece-kuce.