✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ya kafa sabon tarihi

A ranar Talatar da ta wuce ne shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi na wanda…

A ranar Talatar da ta wuce ne shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi na wanda ya fi zura kwallo a raga a gasar zakarun kulob-kulob na Turai da aka fi sani da UEFA Champions League bayan ya zura kwallaye 16 a wasan da kulob din Madrid ya yi da na Bayern Munich da ke Jamus.
Cristiano ne ya zura kwallaye biyu daga cikin hudun da Madrid ta zura a ragar Bayern. Don haka yanzu ya kafa sabon tarihi bayan ya doke tarihin da Lionel Messi na FC Barcelona ya kafa a kakar wasa ta 2011 zuwa 2012 na  zura kwallaye 14 a gasar.  Haka kuma Ronaldo ya shafe tarihin da tsohon dan kwallon AC Milan da ke Italiya mai suna Jose Altafini ya kafa a a kakar wasa ta 1962 zuwa 1963 inda shi ma ya zura kwallaye 14 a raga a gasar.
Ya zuwa yanzu Ronaldo ya zura kwallaye 66 kenan a raga a daukacin wasannin da ya yi a gasar.
dan kwallon da har yanzu yake rike da kambun wanda ya fi zura kwallaye a tarihin gasar kawo yanzu shi ne tsohon dan kwallon Real Madrid Raul da ke da yawan kwallaye kwallaye 71 sai mai biye da shi Lionel Messi mai kwallaye 67 yayin da Ronaldo yake a matsayi na uku da kwallaye 66.