✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ne dan wasa mafi zura kwallaye a 2023 — IFFHS

A watan Yunin bara ne ya zama dan wasa na farko bangaren maza da ya buga wasannin kasa da kasa har 200.

Fitaccen tauraron tamaula, Cristiano Ronaldo, ya kafa tarihin zama dan wasa mafi zura kwallaye a raga a shekarar 2023.

Hukumar Kididdiga da Kundin Tarihin Kwallon Kafa (IFFHS) ce ta tabbatar da wannan bajinta da Cristiano Ronaldo ya yi ta kammala shekarar 2023 a matsayin dan wasan da ya fi zura kwallaye a raga a duniya.

IFFHS ta sahale cewa Ronaldo ya jefa kwallonsa ta 54 kuma ta karshe a shekarar da muka yi ban-kwana da ita a fafatawar da kungiyarsa ta Al Nassr ta lallasa Al-Taawoun da ci 4-1 a gasar lig ta Saudiya.

Ronaldo ya jefa kwallaye 44 a wasanni 50 tun daga watan Janairu, lokacin da ya fara taka leda a Al Nassr ta Saudiya.

Sannan ya jefa kwallaye 10 a wasannin kasa da kasa da ya buga wa Portugal a 2023, abin da ke nuni da cewa, yana da kwallaye 54 cikin wasanni 59 da ya buga jimilla a bara.

Sauran ‘yan wasa da suka zura kwallayen da suka kai 50 a sassan duniya a bara, sun hada da Harry Kane da Kylian Mbappe da dukkaninsu ke da kwallaye 52, sai kuma Erling Haaland mai kwallaye 50.

Ronaldo wanda ya saba kafa tarihi a duniyar tamola, a cikin watan Yunin bara ne ya zama dan wasa na farko bangaren maza da ya buga wasannin kasa da kasa har 200, yayin da ya kasance wanda ya fi yawan kwallaye a wasannin kasa da kasa, inda yake da kwallaye 128.

Har ila yau, Hukumar ta IFFHS ta kuma yaba wa Ronaldo wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar a tarihi saboda wannan gagarumar bajinta da ya yi duk da yana da shekaru 38.