✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ronaldo da Ramos sun sasanta

Manyan ’yan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo da Sergio Ramos sun sasanta bayan kwashe shekara biyu suna gaba da juna. Hakan ya biyo bayan wasan…

Manyan ’yan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo da Sergio Ramos sun sasanta bayan kwashe shekara biyu suna gaba da juna.

Hakan ya biyo bayan wasan kawance na kasa da kasa da Portugal ta buga da Spain a ranar Laraba, wanda ya kare canjaras.

Jaridar Daily Mail ta ruwaito cewar Cristiano Ronaldo da Sergio Ramos sun kwashe shekara biyu ba sa ga maciji.

Sergio Ramos ya wallafa hoton da suka dauka da Ronaldo a shafinsa na zumunta tare da tsohon dan wasan Real Madrid Pepe a dakin canja kayan ’yan wasa.

An ce maganar da Ranoldo ya yi  kan nasarar da Luka Modric ya yi ta Ballon d’Or ce a shekara 2018 ta haddasa gabar.

’Yan wasan biyu sun kwashe shekara tara suna buga kwallon kafa tare a Kungiyar Real Madrid inda suka yi nasarar lashe Gasar Zakarun Turai kafin Ronaldo ya koma Juventus.