Jaridar Tuttosport ta ruwaito cewa Erkut Sogut, dillalin dan wasan tsakiya na kungiyar Arsenal, Mesut Ozil ya tuntubi kungiyar Juventus ta Italiya a kan karbo dan wasan aro.
Sai dai Ozil ba ya gaggawar tafiya ko ina, a yayin da dan wasan ya nuna sha’awar ci gaba da zama a Arsenal har sai kwantaraginsa ya kare.
- Ronaldo ya lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasan Karni
- Matan da suka fi tashe a Najeriya a 2020
- Mutum 23 sun rasu, 33 sun ji rauni a hatsarin tirela a Neja
- Dogo Gide: Mutumin da ya hallaka Buharin Daji
Tun farkon kakar bana kocin Arsenal Mikel Arteta ya daina amfani da Ozil, inda ya cire sunansa a cikin ’yan wasan kungiyar na kakar bana baki daya.
Tuni dai Arsenal ta yanke shawarar raba gari da dan wasan, inda ta amince za ta rika biyan rabin albashinsa na watanni shidan da zai yi a matsayin dan wasan aro a kungiyar da ke Italiya.
Idan Juventus ta amince da karbo aron dan wasan a watan Janairu, zai tafi a kyauta ne, sannan zai sake haduwa da Cristiano Ronaldo, wanda suka buga wa kungiyar Real Madrid tare.
A shekarar 2013 da Ozil ya bar Madrid ya koma Arsenal, masoya Ronaldo da dama sun yi tunanin hakan zai shafi kwazon Ronaldo, kasancewar a lokacin da suke tare, kusan mafi yawan kwallayen Ronaldo daga wajen Ozil ne suke fitowa.