✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ba zai haska a wasan Portugal da Luxembourg ba

Wasu na ganin cewa laifin da Ronaldo ya aikata ya cancanci jan kati.

Cristiano Ronaldo ba zai buga wa Portugal wasan neman shiga gasar kofin nahiyar Turai ba da za ta kara da Luxembourg ranar Litinin.

Dan kwallon Al-Nassr ya karɓi katin gargaɗi a wasan da Portugal ta ci Slovakia 1-0 ranar Juma’a.

Kyaftin ɗin tawagar ta Portugal ya buga kafarsa a fuskar dan kwallon Manchester United, Martin Dubravka, wasu na cewa laifin na jan kati ne.

To sai dai alkalin wasa, Glenn Nyberg ya bai wa tsohon ɗan wasan Real Madrid da Juventus katin gargaɗi, sannan bai je ya duba abin da ya faru ba a VAR.

Kenan ba zai buga karawar ba, sakamakon katin gargadi na uku kenan da aka bai wa tsohon dan wasan Manchester United a fafatawar ta neman shiga gasar kofin nahiyar Turai.

Karon farko da Ronaldo ba zai yi wa Portugal tamaula ba, bayan karawa 10 a jere da ya yi mata, wanda shi ne kan gaba a yawan ci wa tawagar kwallaye.

Rabon da Ronaldo ya kasa buga wa Portugal tamaula tun Nuwambar 2022 a karawar da suka doke Najeriya 4-0 a wasan sada zumunta, sakamakon rashin lafiya.

Ranar Litinin Portugal za ta kece raini da Luxembourg, idan ta yi nasara za ta samu gurbin shiga gasar nahiyar Turai kai tsaye da za a buga a Jamus a 2016.