Fitaccen dan wasan Kungiyar Al Nassr da kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa har yanzu kwallo ba ta kare masa ba.
Dan wasan ya bayyana haka ne bayan ya zura kwallo uku rigis a ragar Kungiyar Al Abha daga cikin kwallo takwas da Al Nassr ta ci a ranar Asabar.
Da wannan nasarar, dan wasan ya kafa wani sabon tarihi, inda ya zama ya zura kwallo uku rigis ko sama da uku sau 65 a tarihin tamaularsa.
Haka kuma wannan ne karo na 35 da ya zura kwallo uku rigis bayan ya haura shekara 30.
A daya bangaren Messi, abokin hamayyarsa ya zura kwallo uku rigis sau shida.
Wannan ya sa ake tunanin zai yi wahalar gaske a samu wanda zai kamo shi, ballanata ya zarce shi.
Aminiya ta ruwaito yadda kwallayen dan wasan ya zura bayan haura shekara 30 suka zarce wasu kwallayen da wasu fitattun ’yan wasa suka zura a tarihinsu na kwallo baki daya.
Haka kuma yanzu dan kwallon yana da kwallo 29 a gasar ta kasar Saudiyya, inda ya kama hanyar lashe kambun wanda ya fi zura kwallo a gasar.
Idan ya samu wannan nasara, zai kafa wani sabon tarihin kasancewar wanda ya lashe kambun wanda ya fi zura kwallo a raga a gasanni hudu daban-daban.
Ya lashe kambun a Gasar Firimiya ta Ingila da Gasar La Liga da Gasar Seria A, sai yanzu kuma a Gasar Saudiyya.