✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Romeo Lavia ya koma Chelsea daga Southampton

Chelsea ta kammala cinikin dan wasan tsakiyar Belgium, Romeo Lavia daga Southampton kan kudi fam miliyan 53 tashin farko. Dan wasan mai shekaru 19 ya…

Chelsea ta kammala cinikin dan wasan tsakiyar Belgium, Romeo Lavia daga Southampton kan kudi fam miliyan 53 tashin farko.

Dan wasan mai shekaru 19 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru bakwai a yarjejeniyar wanda zai iya tashi da karin £5m.

Lavia ya buga wasanni 34 a dukkan gasa a kakar wasan da ta gabata, amma hakan bai hana hana Saints rikitowa daga gasar Firimiyar Ingila zuwa matakin Championship ba.

Liverpool ta yi zawarcin Lavia, amma Southampton ta ki amincewa da tayin kusan fam miliyan 46 da ta yi farkon wannan watan.

Lavia ya zama dan wasa na biyu a cikin wannan makon da ya zabi Chelsea a maimakon tawagar Jurgen Klopp, bayan Moises Caicedo, wanda ya koma Stamford Bridge daga Brighton kan jimillar kudi fam miliyan 115.