Wani magidanci da iyalansu su bakwai sun rasu bayan sun ci wani abinci da aka sarrafa da rogo a ƙauyen Runjin Barmo da yankin Kajiji a Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato
Mai unguwan ƙauyen, Muhammadu Modi Magajin Runjin Barmo, ya bayyana cewa a ranar Laraba ne abincin ya yi aljalin magidancin Mai suna Malam Abubakar da matarsa A’ishatu da ’ya’yansu biyar.
Ya bayyana haka ne a lokacin da Kwamishinar Lafiya ta Jihar Sakkwato, Asabe Balarabe ta kai ziyarar ta’aziyya ƙauyen, bayan aukuwan lamarin.
Mai unguwan ya yaba wa gwamnatin jihar bisa damuwa da ta nuna kan lamarin.
- An sace N50bn daga asusun Gwamnatin Kano —Muhyi
- Manoma 30 sun nutse a hatsarin kwale-kwale a Sakkwato
Kwamishinar Lafiyar ta ce ma’aikatarta za ta gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya faru domin sanar da gwamnan jihar, a ɗauki matakin da ya dace.
A ƙarshe ta ce ma’aikatar ta ɗauki jinin wani matsahi da ya tsallake rijiya da baya bayan cin abincin da ake zargi domin gudanar da gwaje-gwaje.