Roberto Mancini ya zama sabon kocin Saudiyya makonni biyu bayan ya yi murabus a matsayin kocin Italiya.
Mai shekaru 58 ya jagoranci Italiya ta samu nasara a gasar Euro 2020, inda ta doke Ingila a bugun fenareti a wasan karshe a Wembley.
- Yadda shirin sakin madatsar ruwa daga Kamaru ta jefa ’yan Najeriya cikin fargaba
- An kori Ministar Harkokin Wajen Libya kan tattaunawa da Isra’ila
A karkashin Mancini tawagar Italiya ta kafa tarihin buga wasa 37 ba tare da an doke ta ba a jere, amma ta kasa samun gurbin shiga Gasar Kofin Duniya ta 2022.
Ya rattaba hannu kan kwantiragi har zuwa 2027.
Wasansa na farko da zai jagoranta zai zama ranar 8 ga Satumba da Costa Rica a filin wasan St James Park da ke birnin Newcastle.
A Gasar Kofin Duniya da aka yi a bara a karkashin tsohon kociyan tawagar Herve Renard, Saudiyya ta gigita Argentina da ci 2-1 a Qatar amma ta kasa tsallake matakin rukunin farko a gasar.
Mancini ya jagoranci Manchester City ta lashe gasar Firimiyar Ingila na farko a shekara ta 2012, sannan ya jagoranci Fiorentina da Lazio da Inter Milan da Galatasaray da Zenit St Petersburg.
Aminiya ta ruwaito cewa, Mancini ya yi ritaya daga aikin kociyan tawagar Italiya, bayan shekara biyar yana kan aikin.