✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Riz Ahmed: Musulmin farko a karbar kyautar Babban Jarumin Hollywood

Ya kafa tarihin zama Musulmin farko da aka ayyana don samun kyautar babban jarumin Hollywood

Riz Ahmed ya kafa tarihin zama Musulmin farko da aka ayyana don samun kyautar Babban Jarumin fim a kyauttukan fina-finan duniya ta Oscars da za bayar a 2021.

An ayyana Riz Ahmed, haifaffen kasar Birtaniya domin samun kyautar gwarzon babban jarumin fim ne saboda rawar da ya taka a fim din ‘Sound of Metal’.

“Idan ka ji an kira sunanka, abin da ban mamaki! Sai dai kawai na yi hamdala,” inji shi, yayin da yake bayyana farin ciki kan samun damar.

Ya bayyan ba zato, ya bude YouTube yana kallon sunayen wadanda aka ayyana, sai ya ji ashe har da shi, nan take ya sanar da iyalansa suka fara murna.

A ranar 25 ga Afrilu, 2021 za a sanar tare da mika kyaututtukan da wadanda suka samu a rukuni daban-daban a bikin da za a gudanar a Hollywood, kasar Amurka.

Riz, wanda dan asalin kasar Pakistan ya samu wannan damar ce a yayin da aka shekara biyar ana sukar yadda turawa fararen fata suka mamaye kyaututukan na Oscars.

A 2017, Riz ya samu kyautar Emmy a matsayin babban jarumi, saboda rawar da ya taka a fim din ‘The Night Of’.

A shekarar ce kuma ya fito a babban shafin jari New York Times a matsayin daya daga cikin mutum 100 da suka fi shahara a duniya.