Hukumar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce, ta kama mutum 23 dauke da makamai wanda ake zarginsu da cewa, su ne suka tada rikici a karamar hukumar Tsafe lokacin da matasa suka fara zanga-zanga a garin.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara Mista Usman Belel ne ya bayyana wa manema labarai hakan a Gusau babban birnin jihar lokacin da kurar rikicin ta lafa.
Jami’an tsaron sun ce, sun kama matasan dauke da bindigogi lokacin da suke ta kona motoci da gineginen karamar hukumar.