✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin zabe: An gano bama-bamai, mutum 4 sun mutu a Majalisar Amurka

Zaurukan Majalisa sun hade wurin tabbatar da Joe Biden a matsayin zababben Shugaban Kasa

Majalisar Dokokin Amurka ta yi fatali da yunkurin kawo cikas ga tabbatar da nasarar Mista Joe Biden a matsayin Zababben Shugaban Kasar.

Tuni dai Majalisar Wakilan Kasar ta mara wa Majalisar Dattawa baya wurin kalubalantar yunkurin neman soke nasarar Mista Biden zaben da Mista Trump da magoya bayansa suka yi watsi da sakamakonsa.

Hakan na zuwa ne bayan akalla mutum hudu sun mutu baya ga jami’an yan sanda 14 da aka raunata a dauki ba dadin da aka yi tsakanin jami’an tsaro da magoya bayan Shugaba Donald Trump da suka yi kutse a ginin Majlisar Kasar.

Shugaban ’Yan Sandan birnin Washington D.C, Robert Contee, ya ce mamatan sun hada da jami’in dan sanda daya, mace daya da kuma maza biyu a rikicin na ranar Laraba.

Robert Contee ya shaida wa ’yan jarida a cikin tsakar dare cewa runudnar ta gano bom guda biyu, daya a ofishin Kwamitin Jam’iyyar Democrat, daya kuma a na jam’iyyar Republican.

Ya kara da cewa an cafke 52 daga cikin masu tarzomar, yayin da masu zanga-zangar da ’yan sanda suka yi amfani da abun feshi mai tayar da zuciya kafin ’yan sanda su samu ikon fatattakar masu boren.

Trump da magoya bayansa na zargin an yi murdiya a zaben da sakamakonsa ya nuna Mista Biden ne ya yi nasara.

Kutse magoya bayan Mista Trump wanda ya bukace su da su yi maci zuwa ginin Majalisar Dokokin Kasar na Capitol ya sa tilasata Majisar Wakilai dakatar da aikin tabbatar da nasarar Mista Biden.

Lauyan Trump ne neman kawo tsaiko

Jaridar intanet ta The Dispatch ta ce, lauyan Mista Trump, Rudy Giuliani ya gayyato akalla dan Majalisar Datttawa guda daya da nufin kawo tsaiko ga aikin Majalisar Wakilan na tabbatar da nasarar Biden.

Mista left a message ya bar sako ga Dan Majalisar Dattawa daga jam’iyyar Republican, Sanata Tommy Tuberville, magoyin bayan Trump domin jefa kuri’ar farko na kalubalantar kuri’ar da Majalisar Wakilai za ta jefa na tabbatar da sakamakon Jihar Arizona.

Kowace kuri’ar adawa kan jawo wa zaben tsaiko na awanni, yayin da Giuliani ya bukaci Sanata Tommy Tuberville ya kalubalanci sakamakon zaben jihohi 10.