An kashe mutum biyu ’yan kungiyar IMN ta ’yan Shi’a a wani dauki ba dadi da aka yi tsakaninsu da ’yan sanda a Jihar Kaduna ranar Lahadi.
An ji karar harbe-harbe a lokacin da ’yan kungiyar ke yin zanga-zanga, a yunkurin ’yan sanda na tarwatsa taron masu zanga-zangara a kan titin Ahmadu Bello.
“An yi arangama kuma ’yan sanda sun kashe ’yan kungiyarmu guda biyu wasu da dama kuma sun samu raunuka”, inji wani shugaban kungiyar a ganawarsa da Aminiya.
’Yan kungiyar na zanga-zangar ne don neman a sako shugabansu, Shaikh Ibrahim Zakzaky da matarsa Zeenat, da ke tsare tun watan Disamban 2015 bayan wata arangama tsakanin mabiyan malamin da sojoji a Zariya.
Tuni dai gwamnatin Jihar Kaduna ta haramta ayyukan kungiyar ta IMN da duk wani nau’in zanga-zanga a Jihar.
A lokacin da muka nemi jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Muhammad Jagile, ya ce bai samu rahoto game da hakan ba tukuna.
“Na kira Baturen ’Yan Sanda da ke kula da yankin amma bai dau waya ba; babu mamaki yana kokarin shawo kan matsalar ne. Amma da zarar na samu karin bayani zan tuntube ku”, inji shi.