Rasha ta kaddamar da atisayen manyan makaman sojin ruwanta a tekun Bahar Maliya ’yan sa’o’i bayan ta karyata zargin ta da Amurka ta yi na shirin fara kai hari kan Ukraine a kowane lokaci.
Rundunar sojin ruwan Rasha ta fara atisayen ne a ranar Asabar bayan a ranar Juma’a Amurka ta yi wani babban gargadi kan yiwuwar mamayar kasar Rasha a Ukraine, a “kowace lokaci” daga yanzu.
- EU ta umarci jami’anta su fice daga Ukraine
- Amurka ta bukaci ’yan kasarta su gaggauta ficewa daga Ukraine
Ma’aikatar tsaron Rasha ta bayyana cewa, “Akalla jiragen ruwan yaki 30 daga Sebastopol da Novorossiysk sun shiga teku Bahar Maliya bisa ga tsarin atisayen, wadda manufarta ita ce kare gabar tekun Crimea — mastugunin sansanonin sojin ruwan Rasha a Tekun Bahar Maliya — da kuma tattalin arzikin kasar… daga barazanar soji.”
A ranar Juma’a Mashawarcin Tsaron Shugaban Kasar Amurka, Jake Sullivan, ya ce mai yiyuwa Rasha ta fara kai hare-hare ta sama da makamai masu linzami a kan Ukraine, ya kuma bukaci Amurkawa da ke Ukraine din da su fice cikin gaggawa.
Haka kuma wasu kasashen Turai sun bukaci ’yan kasarsu da su fice daga Ukraine.
Moscow ta yi fatali da gargadin Amurka
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha, Maria Zakharova, ta rubuta a shafin Telegram cewa “Rura wutar da fadar White House ke yi ya bayyana bayyana karara fiye da a kowane lokaci. Anglo-Saxon na bukatar yaki. Ko ta halin kaka.
“Tashin hankali, rashin fahimta da kuma barazana shi ne hanyar da suka fi so don magance matsalolin.”
Jakadan Rasha a Amurka, Anatoly Antonov, ya shaida wa mujallar Newsweek cewa, gargadin da Amurka ta yi na da matukar tayar da hankali, kuma ya nanata cewa kasarsa ba za ta kai hari ga kowa ba.
Rasha ta girke dubunnan dakaru a kan iyakokinta da Ukraine a ’yan watannin nan, lamarin da ke kara jawo fargabar cewa tana shirin mamaye makwabciyarta ta tsohuwar Tarayyar Soviet, shekara takwas bayan da ta kwace yankin Crimea daga Ukraine.
Rasha dai ta musanta wannan shirin yayin da take gabatar da jerin bukatu na kasashen Yamma, ciki har da haramtawa Ukraine shiga kungiyar tsaro ta NATO.
A cikin wannan furuci, a watan da ya gabata Rasha ta sanar da wani jerin atisayen sojan ruwa a Tekun Atlantika, Tekun Arctic, Tekun Pasifik da Tekun Bahar Rum da kuma cikin “ruwa da tekun da ke makwabtaka da kasar Rasha.”
Atisayen ya kunshi jiragen ruwa sama da 140, da jiragen sama 60, da kayan aikin soja 1,000 da kuma sojoji sama da 10,000 gaba daya, inji ma’aikatar tsaron kasar a ranar Asabar.
A shekarun baya-bayan nan dai ana zaman dar dar a tekun Black Sea, inda Rasha ke zargin gwamnatin Ukraine da ke goyon bayan kasashen Yamma da kuma kasashen Yamma da yin barazana ga tsaronta a gabar tekun Crimea.
A cikin watan Yunin shekarar da ta gabata ne sojojin Rasha suka yi harbin gargadi kan wani jirgin ruwa na Biritaniya da suka zarga da shiga cikin ruwanta, ikirarin da Birtaniyya ta musanta.
A yayin da ake atisayen sojan ruwa, ana kuma gudanar da atisayen soji da dama na kasar Rasha tare da kawancen Belarus, ta hannun damar Rasha.