Farashin danyen man fetur da na iskar gas ya hauhawa sakamakon fargabar da rikicin Rasha da Ukraine ke haifarwa game da jigilar makamashin a fadin duniya.
Danyen man da aka fi amfani da shi a duniya na samfurin Brent, ya yi tashin gwauron-zabi fiye da kowane lokaci cikin shekara bakwai, inda aka fara sayar da ganga a kan Dala 99.38 a ranar Talata.
- Mataimakin gwamnan Zamfara ya ki bayyana gaban kwamitin da ke bincikarsa
- Kwankwaso ya jagoranci taron kaddamar da sabuwar kungiyar siyasa
Sai dai kamfanin makamashi na Birtaniya RAC, ya yi gargadin cewa lamarin zai iya sake harzuka farashin mai a Birtaniya bayan ya kai fan 149.12 kan kowace lita a ranar Lahadi.
Kasashen turai sun yi barazanar sanya wa Rasha takunkumi, duk da cewar kasar ita ce mafi arzikin iskar gas a duniya.
Rasha ta umarci dakarunta su shiga yankuna biyu na Ukraine wadanda suka ayyana kansu a matsayin masu ‘yancin kai, bayan ta amince da ikirarin nasu.
A ranar Talata, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya ba da umarnin dakatar da gina bututun iskar gas tsakaninsa da Rasha mai suna Nord Stream 2 wanda aka tsara zai samar da gas din kai-tsaye daga Rasha zuwa Jamus.
Tuni lamarin ya sanya farashin gas din ya tashi sakamakon haka.