✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin Ukraine: Farashin gangar mai ya haura Dala 113

Cikin ’yan sa'o'i a ranar Larbar ce Brent ya karu da akalla Dala uku daga Dala 110.18 ya kai Dala 113.

Farashin gangar danyen mai a kasuwar duniya ya kara yin tashin gwauron zabo inda ya haura Dala 110 a sakamakon mamayar Rasha a kasar Ukraine.

An wayi garin Laraba da farashin gangar danyen mai samfurin Brent ya karu zuwa Dala 113, na WTI kuma Dala 110.50 — kuma rabon da hakan ta faru sun a shekarar 2014.

Cikin ’yan sa’o’i a ranar Larbar ce Brent ya karu da akalla Dala uku daga Dala 110.18 ya kai Dala 113.

Tun bayan barkewar yakin Rasha a Ukraine a ranar Alhamis da ta gabata ake ta samun hauhawar farashin mai a kasuwar duniya.

Hakann na faruwa ne duk da cewa takunkumin karya tattalin arziki da kasashen Yamma suka kakaba wa Rasha bai taba bangaren makamashinta ba, wato mai da iskar gas.

Matakan karya tattalin arzikin da suka hada da kwace kadarorin Rasha da katse huldar kasuwanci da sauran mu’amala da kasashen Yamman suka dauka ya haifar da fargabar samun karacin mai a kasuwar duniya.

Bukatar mai dai sai kara karuwa yake yi, a yayin da mana’antu da sauran kamfanonin duniya suke kokarin farfadowa gami da ci gaba da harkokinsu, bayan kulle da asarar da suka tafka a sakamakon bullar annobar COVID-19.

Rasha dai ita ce kasa ta biyu wajen yawan arzikin mai a duniya, kuma ita ce ja-gaba wajen samar da iskar gas ga kasashen Turai.

A safiyar Laraba Rasha ta yi ikiracin kwace birinin Kherson da ke Kudancin kasar Ukraine, inda ta shafe kwana shida tana luguden wuta.

“Rundunar tsaron Rasha ta kwace ikon yankin Kherson kuma yanzu yana hannunta,” inji kakakin Ma’aikatar Tsaron Rasha, Igor Konashenkov.