Shugaban Rasha, Vladimir Putin ya kare hare-haren da kasar ke kai wa kasar Ukraine, inda ya zargi Ukraine da kasashen Yamma da neman rikici, a yayin da yake kokarin yin amfani da bikin tunawa da nasarar yakin duniya wajen neman goyon bayan al’ummar kasar.
Gidan rediyon BBC ya ce Shugaba Putin ya bayyana haka ne a wajen faretin shekara-shekara don tunawa da ranar nasarar Tarayyar Soviet a kan sojojin Nazi na Jamus, inda ya ce dakarun Rasha da ke Ukraine suna kare martabar kasarsu ce, yana mai bayyana rikicin da ci gaban Yakin Duniya na Biyu.
- Takarar Emefiele: INEC za ta kwashe kayan zabe daga CBN
- Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan ya rasu
Shugaba Putin ya shaida wa sojin Rasha da ke fagen fama a Ukraine cewa suna yaki ne don tabbatar da makomar kasarsu, don kada kowa ya manta da darusan Yakin Duniya na Biyu.
Putin ya yi ta kokarin danganta yakin Ukraine da abin da Rashawa ke kira ‘gagarumin yaqin kishin kasa’ ta wajen bayyana hukumomin Ukraine a matsayin masu akidar Nazi a wannan zamani.
Bai yi wata sanarwa muhimmiya ba a yayin jawabin nasa, duk kuwa da yadda rahotanni suka nuna cewa yana iya amfani da bikin wajen gabatar da rincabewar rikicin.
A maimakon haka, Putin ya ci gaba da kare abin da ya kira sintirin soji a Ukraine, yana mai cewa abokanta da Turai na shirya kullalliyar mamayar yankunan Rasha na tarihi, ciki har da yankin Donbas da Kirimiya da ke amfani da harshen Rashanci, wadanda Rashar ta mamaye a shekarar 2014.
Putin ya ce Rasha ba ta da wani zabi face mayar da martani a kan abin da take tunani kasashen Yamma za su iya yi mata ta hanyar mamaya, yana mai bayyana shi a matsayin mataki mafi dacewa da ya kamata ’yantacciyar kasa mai karfi ta dauka.
A martanin Shugaban Qasar Ukraine, Mista Volodymyr Zelensky ya ce Shugaban Kasar Rasha Mista Viladmir Putin yana maimaita ta’asar da Mista Adolf Hitler na kasar Jamus ya yi ne kawai.
Shugaba Vlodymyr Zelensky ya ce, luguden wuta da sojojin kasar Rasha suke yi musu a birane da kwashe mutanensu fararen-hula suna tilasta su komawa cikin kasar Rasha ba ya da bambanci da miyagun ayyukan da ’yan Nazi suka tafka a lokacin Yakin Duniya na Biyu.