An hallaka jami’an ’yan sanda biyu a sabon rikicin kabilanci tsakanin al’ummar Tibi da Jukun a Jihar Taraba.
’Yan sandan sun rasu ne yayin da wasu suka samu raunukan bindiga a harin da ’yan sa kai suka kai da sanyin safiyar Laraba a garin Chanchangi na Karamar Hukumar Takum ta Jihar Taraba.
- Mayakan Boko Haram sun kai hari Geidam
- ’Yan sanda sun yi wa ’yan bindiga luguden wuta a Zamfara
- Ba’amurkiyar da ta kashe dan Najeriya ta shiga hannu
- Tsohon Sarkin Kano ya magantu kan dakatarwar da aka yi wa Sheikh Abduljabbar
Wani mazaunin Chanchangi ya ce shaida wa Aminiya cewa mahara dauke da muggan makamai daga Jihar Binuwai sun far wa garin ne suna harbi kan mai uwa da wabi, inda suka kashe ’yan sandan kwantar da tarzoma biyu suka raunata wasu da dama ciki har da kananan yara.
Ya ce yayin da harin ya jefa ’yan garin cikin firgici, mutane da dama musamman mata da kananan yara sun tsere, yayin da wasu maza suka yi dauki ba dadi da su da maharan.
Mutumin ya ce da zuwan maharan sai suka wuce zuwa fadar wani basarake za su shiga amma mutanen garin suka ja daga suka hana su, wanda a artabun ne aka jikkata wasunsu.
Ya ce daga baya an turo ’yan sanda garin suka fatattaki maharan, yayin da wasu mazauna ’yan kabilar Tibi suka tsallaka suka koma Jihar Binuwai.
Wata majiya a garin Takum ta ce an kai wasu daga cikin wadanda aka raunata Babban Asibitin Takum inda ake jinyar su.
A kusa da garin Chanchangi ne ’yan ta’adda suka yi garkuwa da matasan Takum 26 mako biyu da suka gabata.
Harin da ake zargin yaran tsohon dan ta’addan Jihar Binuwai, Gana ne suka kai, ya dawo da zaman doya da manja tsakanin ’yan kabilar Tibi da makwabatansu Jukunawa a Jihar Taraba.
Kakakin ’yan sandan Jihar, ASP Leha Refrom ya tabbatar ta da aukuwar harin da kuma kashe dan sanda daya tare da jikkata kananan yara hudu.