✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Sudan: Masar ta ba da lamunin ketarewa da daliban Najeriya

Buhari ya nemi alfarma daga wajen takwaransa na Masar, Abdel Fattah El-Sisi.

Gwamnatin Masar ta ce ta yarda a kwashe daliban Najeriya da ke tsere wa fadan da ake yi a Sudan ta kasarta.

Shugabar Hukumar Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Ketare NiDCOM, Abike Dabiri-Erewa ce ta tabbatar da wannan lamari.

A cewarta, Gwamnatin Masar ta bayar da wannan lamuni ne bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi alfarma daga wajen takwaransa na Masar din, Shugaba Abdel Fattah El-Sisi

Ta bayyana cewa Masar ta ce za ta yarda da wannan muradi ne kawai idan Gwamnatin Najeriyar ta cika wasu tsauraran sharudda.

Da yake zantawa da BBC, Jakadan Najeriya a Masar, Nura Abba Rimi ya fayyace sharuddan da Gwamnatin Masar ta gindaya gabanin cimma wannan yarjejeniya.

Ambasada Nura Abba Rimi ya ce sharuddan da kasar ta Masar ta gindaya sun hadar da cewa dole ne sai Najeriya ta bayyana tsarin da ta yi na jiragen da za su sauka a kasar domin kwashe daliban.

Haka kuma Gwamnatin Masar ta nemi a bayyana girman jiragen saman da za su yi jigilar tare da tabbatar da cewa za a zarce da daliban kai-tsaye daga bakin iyakar kasar zuwa filin jirgi da aka yarje.

Baya ga wannan, an bukaci cikakken jerin sunayen mutanen da za a kwashe ta kasar da kuma lambar fasfo dinsu na tafiye-tafiye da sauran cikakkun takardun tafiya.

Bugu da kari, ta bukaci kasancewar jami’an gwamnatin Najeriya a wuraren kwashe daliban da kuma motocin safa da za su kwashi daliban daga bakin iyaka zuwa filin jiragen sama.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Hukumar Kula da ’yan Najeriya Mazauna Ketare ta sanar da cewa hukumomin Masar sun ki bude kan iyakarsu ga daliban Najeriya wadanda ke guje wa rikicin da ke faruwa a Sudan.

Hukumar ta NiDCOM ta ce yanzu haka akwai jirgin sojin Najeriya da ke girke a birnin Aswan, kuma a cewar ta, jirgin ba zai baro birnin ba sai ya dauki daliban na Najeriya.

Najeriya dai na da dalibai sama da 500 wadanda suka makale a bakin iyakar kasar ta Masar, suna jiran izinin shiga domin kwashe su zuwa gida.

A baya kasar Habasha ta hana daliban Najeriya bi ta kasarta domin tsere wa fadan na Sudan, wani abu da ya janyo suka daga bangarori da dama.

Lamarin na faruwa ne a yayin da dai Gwamnatin Najeriya ke fafutikar ganin yadda za ta iya kwaso dubban dalibai da sauran al’ummarta daga Sudan inda fada ya barke a makon jiya.

Bayanai na cewa wasu daliban na kan hanyarsu ta zuwa kan iyakar Sudan da Saudiyya, inda ake sa ran za su tsallaka zuwa cikin kasar kafin a kwashe su zuwa gida.

Fada ya barke ne tsakanin bangarorin dakaru masu biyayya da manyan jami’an sojin Sudan biyu.

Tuni kasashe da dama suka kwashe al’ummarsu domin gudun kada yakin ya rutsa da su.

Kasashen duniya dai na ci gaba da rige-rigen ganin sun kwashe ’yan kasarsu daga Sudan, bayan ballewar fada tsakanin dakaru masu mubaya’a ga manyan hafsoshin sojin kasar biyu.